Tsohon shugaban jam’iyyar APC na jihar arewa ya sauya sheka zuwa PDP

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na jihar arewa ya sauya sheka zuwa PDP

  • Tsohon shugaban jam’iyyar APC na Jihar Filato, Hon. Latep Dabang da daruruwan mabiyan sa sun sauya sheka inda suka koma jam’iyyar PDP daga APC
  • Dama an dakatar da shi ne da farko sannan aka cire shi daga mukamin sa bayan samun wasu matsaloli wanda daga nan ba sa sake jin duriyar sa ba
  • Sai dai daga bayan nan ne aka samu bayanai akan yadda ya gana da wasu jiga-jigai na jam’iyyar PDP kafin ya fito ya bayyana batun komawar sa jam’iyyar

Jihar Filato - Tsohon shugaban jam’iyyar APC na Jihar Filato, Hon. Latep Dabang da daruruwan mabiyan sa sun koma jam’iyyar PDP daga jam’iyyar APC, Vanguard ta ruwaito.

Dama an dakatar da Dambang ne sannan aka cire shi daga mukamin sa bayan wasu matsaloli sun auku wanda tun daga lokacin ba a sake jin komai daga wurin sa ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: APC ta hadu da cikas yayin da manyan jiga-jiganta 4 da magoya bayansu suka koma PDP

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na jihar arewa ya sauya sheka zuwa PDP
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na Filato ya sauya sheka zuwa PDP. Hoto: Vangaurd
Asali: Twitter

Sai dai an samu labarai akan yadda ya gana da wasu manya a jam’iyyar PDP kafin ya bayyana batun sauya shekar sa a ranar Talata.

Akwai sauran jiga-jigan APC da suka koma PDP a jihar

Sauran wadanda suka sauya shekar tare da shi sun hada da tsohon dan majalisar jihar, Hon. Nanpon Tom da tsohon mataimakin sakataren jam’iyyar na jihar, Hon. Binkur N. da saura mabiyan su.

An amshe su ne a ranar Talata yayin wani gangami na Langtang na 2022 wanda suka yi wa take da: “Babbar tafiya.”

Yayin tattaunawa da manema labarai bayan kammala taron a Langtang North township Stadium, Hon. Latep Dabang ya ce PDP zata ci nasara a jihar a zaben 2023 inda yace duk wasu mutane masu rinjaye a APC sun koma PDP.

Kara karanta wannan

'Ka ga haske', Lawan ya jinjina wa Bwacha, Sanatan Taraba da ya fice daga PDP ya koma APC

Latep ya ce Jihar Filato na gab da bankwana da APC

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, Latep ya bayyana yadda suke hararo nasara a zaben mazabar Pankshin ta kudu da mazabar Bassa da Jos ta arewa wanda za a yi a ranar 28 ga watan Fabrairun 2022 inda yace yana da tabbacin PDP za ta lashe zaben.

Kamar yadda ya ce:

“Ina da tabbaci akan cewa PDP ce zata lashe zabukan babu tantama. Mutanen Filato sun kusa yin bankwana da APC.”

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Chris Hassan ya bayyana farincikin sa akan yadda ake ta komawa PDP inda yace suna sa ran nasara a gabadaya zabukan da za a yi a shekarar 2023.

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hotuna: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu, fitaccen sanata ya bar PDP ya shigo APC

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164