Da dumi-dumi: APC ta hadu da cikas yayin da manyan jiga-jiganta 4 da magoya bayansu suka koma PDP

Da dumi-dumi: APC ta hadu da cikas yayin da manyan jiga-jiganta 4 da magoya bayansu suka koma PDP

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta rasa wasu manyan jiga-jiganta a jihar Filato, inda suka sauya sheka zuwa PDP
  • Daga cikin wadanda suka fice daga jam'iyyar harda tsohon shugaban jam'iyyar a jihar Filato, Hon. Latep Dabang da kuma tsohon shugaban masu rinjaye a Majalisar dokokin jihar
  • Sun sauya shekar ne tare da dubbin magoya bayansu a yayin wani gangamin jam'iyyar adawar

Plateau - Tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Filato, Hon. Latep Dabang ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Leadership ta rahoto.

Rahoton ya kuma kawo cewa tsohon shugaban masu rinjaye a Majalisar dokokin jihar Filato, Hon. Henry Yenkwap ma ya fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP a jihar.

Da dumi-dumi: APC ta hadu da cikas yayin da tsohon shugabanta da shugaban masu rinjaye suka koma PDP
Da dumi-dumi: APC ta hadu da cikas yayin da tsohon shugabanta da shugaban masu rinjaye suka koma PDP Hoto: @HonAhmedWase
Asali: Twitter

Hakazalika, tsohon shugaban karamar hukumar Quanpan, Hon. Isaac Kwalu da tsohon dan majalisar dokokin Filato, Hon. Nanpon duk sun tarkata sun koma PDP, rahoton The Eagle.

Kara karanta wannan

2023: Hotunan ziyarar da manyan jiga-jigan PDP suka kaiwa tsohon shugaban kasa, IBB

Tsoffin mambobin na APC wadanda suka sauya shekar tare da magoya bayansu sun samu tarba daga jam’iyyar adawar a yayin wani gagarumin gangami da aka gudanar.

2023: Hotunan ziyarar da manyan jiga-jigan PDP suka kaiwa tsohon shugaban kasa, IBB

A wani labarin, mun kawo cewa manyan jiga-jigan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun kaiwa tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin sojoji, Ibrahim Badamasi Babangida, ziyarar bangirma.

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, ne ya jagoranci tawagar zuwa gidan tsohon shugaban kasar da ke unguwar Hilltop a garin Minna, babban birnin jihar Neja, a ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu.

A cikin hotunan wanda jaridar Leadership ta wallafa, an gano tsohon sanata mai wakiltan Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Dino Melaye a cikin tawagar.

Kara karanta wannan

Babbar magana ta fito: Shugaban PDP na jihar Kudu ya sauya sheka zuwa APC, ya fadi sirri

Asali: Legit.ng

Online view pixel