Da Dumi-Dumi: Gwamnati Ta Rufe Ofishin Hukumar Lantarki Saboda Yanke Wutar Ofishin Gwamna

Da Dumi-Dumi: Gwamnati Ta Rufe Ofishin Hukumar Lantarki Saboda Yanke Wutar Ofishin Gwamna

  • Gwamnatin Jihar Oyo ta fara rufe ofisoshin hukumar lantark na Ibadan, IBEDC, bisa ikirarin cewa ba su biya haraji da wasu kudade ba
  • Hakan na zuwa ne bayan hukumar lantarkin da datse wutan Sakatariyar Gwamnatin Jihar wacce ke hade da ofishin gwamna
  • Hukumar ta IBEDC ta yi ikirarin cewa rufe ofisoshinta saba ka'aida ba kuma wani mataki kawai na musguna mata a maimakon gwamnatin jihar ta biya bashin da ake binta

Oyo - Hukumar rarraba wutar lantarki na Ibadan, IBDEC, ta ce Gwamnatin Jihar Oyo, ba bisa ka'ida ba, ta rufe mata ofisohinta saboda yanke wutar lantarki na Sakatariyar Jihar wanda ke hade da Ofishin Gwamna, rahoton Punch.

Kamfanin lantarkin ta ce tana bin gwamnatin jihar bashin Naira miliyan 450 hakan yasa ta yanke wutar sakatariyar don ba a biya bashin ba amma gwamnatin jihar sai ta mayar da martani ta hanyar rufe ofisoshinta da sunan ana binsu bashi.

Kara karanta wannan

Almundahanar kudin makamai N13.8bn: An hana tsohon shugaban Soji fita kasar waje

Da Dumi-Dumi: An rufe ofisoshin hukumar lantarki saboda yanke wutan ofishin gwamnan Oyo
Gwamnati ta rufe ofishin hukumar lantarki bayan ta yanke wutar ofishin gwamna. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kamfanin, John Ayodele, a ranar Laraba, da mai magana da yawun hukumar IBEDC, Busolami Tunwase ya fitar.

Kamfanin ta ce gwamnatin jihar ta yi ikirarin cewa tana bin IBEDC bashin kudaden haraji da wasu kudaden hakan yasa ta rufe ofishinta, amma Ayodele ya ce akwai alamar tambaya game da ikirarin.

Ayodele ya yi bayanin cewa kafin su yanke wutar, kamfanin sun bi hanyoyi daban-daban domin ganin an biya kudin ciki har da rubuta wasika da kuma taro amma duk hakan bai sa an biya ba.

Wani sashi na sanarwa ya ce:

"Hukumar IBEDC na sanar da abokan huldarta ramuwar gayya da saba doka da Gwamnatin Jihar Oyo ta yi saboda dimbin bashin da ake bin ta.

Kara karanta wannan

Mun shirya komawa wani sabon yajin-aikin da babu ranar dawowa inji 'Yan Kungiyar ASUU

"A ranar Laraba 9 ga watan Fabrairun 2022 gwamnatin Oyo ta fara rufe ofisoshinmu a jihar kan wasu bashin haraji da wasu kudade da aka bijiro da su ba tare da sanarwa ba.
"Akwai alamar tambaya game da batun haraji da sauran kudaden a yanzu.
"Muna bin gwamnatin Oyo bashn Naira miliyan 450 cikin shekaru uku.
"Babu kasuwancin da za ta cigaba idan ana rike mata bashi irin haka, ba mu da zabi sai yanek wutar sakatariyar gwamnatin Oyo, abin damuwa kuma sai gwamnati ta fara rufe ofisoshin mu a maimakon biyan bashin."

Shugaban IBEDC ya roki Gwamna Makinde ya saka baki

Shugaban na IBEDC, Ayodele ya yi kira ga Gwamna Seyi Makinde ya saka baki a batun domin kada abin ya shafi mazauna jihar da masu kasuwanci.

Kamfanin na IBEDC ta yi ikirarin cewa ba da niyya mai kyau gwamnati ta ke rufe mata ofisoshinta ba.

Ana bin kowanne ɗan Najeriya bashin N64,684 bisa basukan da ƙasar ta ci a ƙasashen waje

Kara karanta wannan

Kaduna: Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindiga, sun kubutar da wadanda aka sace

A wani labarin, kun ji cewa bisa yawan ‘yan Najeriya da kuma yawan basukan da ake bin ta, kowa ya na da N64,684 a kan sa.

Kamar yadda kowa ya san yawan bashin da Najeriya take ta amsowa daga kasashen ketare, yanzu ko wanne dan Najeriya ya na da bashin $157 ko kuma N64,684 a kan sa.

Bisa wannan kiyasin, masanin tattalin arzikin kasa, Dr. Tayo Bello ya bayyana damuwar sa akai inda ya ce duk da zuzurutun basukan, babu wasu abubuwan ci gaba da aka samar wadanda za su taimaka wurin biyan basukan kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164