Buhari: Ci Gaban Najeriya Ya Dogara Ne Ga Kimiyya Da Fasaha

Buhari: Ci Gaban Najeriya Ya Dogara Ne Ga Kimiyya Da Fasaha

  • Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yi imani ci gaban Najeriya dungurungun ya dogara ga ilimin kimiyya da fasaha
  • Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Talata yayin bayar da lambar yabo ta kasa na shekarar 2020 da 2021 ga ‘yan Najeriya 3 wadanda suka yi bajinta kan harkar lafiya da kimiyya
  • Wadanda suka amshi lambar yabon sun hada da Dr Oluyinka Olurotimi Olutoye, ta lafiya (2020), marigayi Farfesa Charles Ejike Chidume, kimiyya (2020), sai Farfesa Godwin O. Samuel Ekhaguere, ta kimiyya (2021)

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana imaninsa akan cewa nan gaba kadan Najeriya za ta dogara ne ga ilimin kimiyya da fasaha, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Masu son kujerar Buhari basu san dumin da ke tattara da ita ba, inji Sanusi

Buhari ya fadi hakan ne a ranar Talata a Abuja cikin gidan gwamnati yayin mika lambar yabo ta Najeriya ta shekarar 2020 da 2021 ga ‘yan Najeriya uku wadanda suka yi bajinta a bangarori daban-daban na lafiya da kimiyya.

Buhari: Ci Gaban Najeriya Ya Dogara Ne Ga Kimiyya Da Fasaha
Buhari Ya Ce Ci Gaban Najeriya Ya Dogara Ne Ga Kimiyya Da Fasaha. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Wadanda suka amshi lambar yabon sun hada da Dr Oluyinka Olurotimi Olutoye, na lafiya (2020); marigayi Farfesa Charles Ejike Chidume, na kimiyya (2020) da kuma Farfesa Godwin O. Samuel Ekhaguare, na kimiyya (2021).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari ya ce ‘yan Najeriya na fatan wadanda aka ba lambar yabon zasu samar da ci gaba mai yawa ga kasa

Kamar yadda shugaban kasa ya ce musu:

“Ku dinga jajircewa wurin zama madubin dubawa ga yaran Najeriya masu tasowa, ku dinga tunatar da su cewa ci gaban Najeriya ya dogara ne da kokarin mu wurin bunkasa kasa musamman ta kimiyya da fasaha.”

Kara karanta wannan

Buhari ya kawo duk cigaban da ake bukata, abu ɗaya ya rage wa yan Najeriya, Minista ya magantu

Dama tuni shugaban kasa ya bayyana yadda aka fara bayar da lambar yabon Najeriya tun shekaru 43 da suka gabata inda yace mutane ukun da aka ba sun shiga cikin jerin mutane 79 da aka taba ba lambar yabon.

A wata takarda wacce Buhari ya saki ta kakakinsa, Femi Adesina, kamar yadda Daily Trust ta nuna, ya kara da cewa muhimmancin lambar yabon ya kai ga cewa kasa tana fatan sabbin wadanda aka ba su samar da ci gaba mai yawa kamar yadda na baya suka yi.

Yayin taya su murna, ya yaba da wadanda aka ba lambar yabon shekarar 2020 akan hakuri da juriyarsu wanda ya janyo suka jira tsawon shekaru biyu sakamakon bular annobar COVID-19 a shekarar 2020.

‘Yan uwa da abokan arzikin wadanda aka ba lambar yabon sun nuna jin dadin su a majalisar da aka yi taron, sannan sun bukaci matasa su yi aiki tukuru wurin samar da ci gaba mai yawa ga kasar nan.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa

Daya daga cikin su ya rasu bayan an zabe shi

Ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, Sanata George Akume ya ce an zabi mutane ukun da suka amshi lambar yabon ta 2020 da 2021 cikin fiye da mutane 1,200 da suka nemi lambar yabon wacce shugabancin kwamitin NNOM suka zabe su sakamakon duba ayyukan su.

A cewarsa:

“Akwai matukar muhimmanci a sanar da yadda Farfesa Charles Ejike Chidume ya rasu bayan an zabe shi, kuma shugaban kasa ya yarda da a bayar da lambar yabon duk da ba ya da rai.”

Ministan ya yi kira ga jami’o’in Najeriya da su mike wurin yin bincike tukuru don samar da mafita ga matsalolin da Najeriya take fuskanta musamman a wannan zamani na COVID-19.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164