Kisan Hanifa: Rashin lauya da zai kare su Tanko ya janyo jinkiri a shari'ar da ake musu
- An samu koma-baya dangane da shari’ar kisan Hanifa Abubakar mai shekaru 5, saboda rashin samun lauyan da zai kare Abdulmalik Tanko da wadanda ake zargin sun hada kai da shi wurin yin aika-aika, a gaban kotu
- An gurfanar da Abdulmalik tare da Hashimu Isyaku da Fatima Bashir bisa zargin su da aikata laifuka biyar, cikin su akwai hada kai wurin yin aika-aika, garkuwa da mutane da kisa
- Yayin da aka gabatar da karar gaban alkali Usman Na’abba, ba tare da lauyan da zai kare su ba, hakan ya sa sun bukaci kotun ta taya su rokon gwamnatin Jihar Kano don ta samar musu lauya
Kano - Bayan gurfanar da Abdulmalik Tanko tare da wadanda ake zargin sun hada kai don halaka Hanifa Abubakar ‘yar shekara 5, a ranar Litinin, an samu koma-baya dangane da shari’ar kasancewar wadanda ake zargin ba su da lauyan da zai kare su, Vanguard ta ruwaito.
An gurfanar da Abdulmalik tare da Hashimu Isyaku da Fatima Bashir bisa zargin su da laifuka biyar, wadanda suka hada da bayar da hadin-kai wurin yin aika-aika, garkuwa da mutane da kuma aikata kisan kai wanda laifukan sun ci karo da sashi na 97, 274, 277 da 221 na penal code.
Yayin da aka gabatar da shari’ar gaban alkali Usman Na’abba, inda ba su da lauya mai kare su, sun bukaci kotu ta roki gwamnatin Jihar Kano ta sama musu lauyan da zai kare su.
Vanguard ta bayyana yadda kwamitin da zara zartar da hukunci wacce antoni janar na jihar kuma kwamishinan shari’a, Musa Abdullahi Lawan ke jagoranta ta bukaci kotu ta bayar da mako daya don a samar wa wadanda ake zargin lauyan da zai kare su.
Lawan ya ce an riga an yanke wa wadanda ake zargin hukunci
A cewar Lawan:
“Ma’aikatar shari’a ta riga ta yanke hukunci ga Abdulmalik da sauran mutane biyun da ake zargi. Kuma ya kamata a karanto hukuncin a gaban kotu a zaman yau.
“Sai dai ba a samu mai kare su ba. Wanda hakan babban laifi ne a kundin tsarin mulki wanda ya ce ba ya kamata a yanke wa mutum hukunci ba tare da ba shi damar kare kansa ba.
“Kun ji yadda kotu ta bukaci su gabatar da lauya suka ce ba su da shi. Daga nan suka bukaci gwamnatin jihar su ta samar musu lauya. Yanzu muka san hakan. Hakan yasa muka ba su dama don a samar musu da lauya.”
An dage sauraron shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Fabrairu
A cewar sa, an kara musu mako daya, zuwa ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 don su samu lauya yadda za a yanke hukunci cikin sauki.
Ya kara da tabbatar da cewa ma’aikatar shari’a ta damu kuma a shirye take da ta zartar da hukunci. A shirye suke tsaf da su gabatar da duk wasu shaidu.
Alkali mai shari’a, Justice Na’abba ya amince da bukatar wadanda ake zargin inda ya dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Fabrairun 2022.
Idan ba a manta ba, wanda ake zargi da kisan Hanifa, Abdulmalik tare da sauran wadanda suka hada kai da shi sun gurfana ne a gaban kotun majistare amma aka mayar da shari’ar zuwa babbar kotu saboda kotun majistaren ba ta da damar yanke hukunci akan irin wadannan laifukan.
Asali: Legit.ng