Yanzu-yanzu: Mun fara shawara kan mikawa gwamnatin Amurka Abba Kyari

Yanzu-yanzu: Mun fara shawara kan mikawa gwamnatin Amurka Abba Kyari

  • Ministan Shari'a ya yi tsokaci kan inda aka kwana kan lamarin hazikin dan sanda, Abba Kyari
  • Malami ya ce ana tattaunawa da gwamnatin Amurka kan abubuwa da dama, ciki har da yiwuwar mikashi gareta
  • Tuni an umurci Sifeto Janar na yan sanda ya kaddamar da sabon bincike kan alakar Abba Kyari da dan damfara Hushpuppi

Abuja - Antoni Janar na tarayya, Abubakar Malami, ya bayyana cewa Gwamnatin Amurka da Najeriya na tattaunawa kan yiwuwan mika dakataccen jami'an dan sanda DCP Abba Kyari bisa zargin hannu cikin almundahanan $1m.

Abubakar Malami ya bayyana cewa lallai akwai kamshin gaskiya cikin tuhumar da ake yiwa Abba Kyari.

Malami ya bayyana hakan ne yayin hira a shirin 'Politics Today' na tashar ChannelsTV ranar Litinin.

Malami yace:

"Akwai lamura da dama da ake tattaunawa kan yiwuwan mikashi ga Amurka. Anan muke bukatan hadin kai."

Kara karanta wannan

Idan NDLEA ta gama bincike kan Abba Kyari, za'a mika shi ga gwamnatin Amurka

"A iya sani na, bangarorin biyu na tattaunawa, suna hada kai kan lamarin bincike, mikashi ga Amurka, da sauran su."
"Lallai an tabbatar da kamshin gaskiya cikin zargin da ake masa kuma akwai yiwuwan gurfanar da shi da kamashi da laifi idan doka ta kamashi da laifi."

Abba Kyari da Hsuhpuppi
Yanzu-yanzu: Mun fara shawara kan mikawa gwamnatin Amurka Abba Kyari Hoto: Punch
Asali: Facebook

Hukumar aikin yan sanda PSC ta ce a sake sabon bincike kan Abba Kyari

Hukumar aikin yan sanda (PSC) ta umurci Sifeto Janar na yan sanda, Usman Baba Alkali, ya kaddamar da sabon bincike kan alakar dake tsakanin dakataccen jami'i Abba Kyari, da dan damfara, Abbas Ramon, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

A cewar Sahara Reporters, wannan umurni ya biyo bayan shawarar da Antoni Janar na kasa kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya bada.

Kara karanta wannan

Sunayen abokan harkallar Kyari 2 da jami'an NDLEA dake da hannu a safarar miyagun kwayoyi

Rahoton yace a ranar Laraba, 26 ga Junairu, Antoni Janar yace hujjojin dake cikin takardan binciken da aka gudanar basu da karfin da za'a kama Abba Kyari da laifi a kotu.

Abba kyari ya amsa tambayoyi kan zargin da ake masa

An samu bayanai akan yadda Kyari ya amsa tambayoyi akan zarginsa da damfarar dala miliyan 1.1 da wani fitaccen dan Instagram, Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi.

FBI ta zargi yadda Hushpuppi ya hada kai da Kyari wurin kama wani abokin harkarsa, Chibuzo Vincent, don barazanar fallasa damfarar dala miliyan 1.1 da ya yi ga wani dan kasuwar Qatar.

FBI ta Amurka ta ce Hushpuppi ya tura dala 20,600 cikin asusun bankin Kyari.

Sakamakon haka ne PSC ta dakatar da Kyari sannan ta samar da kwamiti na musamman don bincike (SIP) akan gano ko Kyari ya na da hannu a damfarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng