Da Dumi-Dumi: Ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa da yan bindiga suka sace ya kubuta

Da Dumi-Dumi: Ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa da yan bindiga suka sace ya kubuta

  • Dan uwan tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan da aka yi garƙuwa da shi kwanakin baya ya kubuta daga hannun yan bindiga
  • A ranar 24 ga watan Janairu. wasu masu garkuwa da ba'a san ko suwaye ba suka yi awon gaba da Jephthah Robert Yekorogha
  • Kanin Mista Yekorogha, shi ya tabbatar da dawowar ɗan uwansa a wata gajeruwar sanarwa da ya fitar yau

Bayelsa - Ɗan uwa ga tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Jonathan, da aka yi garkuwa da shi kwanakin baya ya shaki iskar yanci bayan shafe kwana 14 a hannun yan bindiga.

Jaridar Punch ta rahoto cewa mahara sun yi awon gaba da Jephthah Robert, a ƙofar gidinsa dake Biogbolo-Epie, Yanagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Tun a ranar 24 ga watan Janairu, 2022, yan bindigan suka yi garkuwa da fitaccen ɗan siyasan, kuma ya shafe kwanaki 14 a hannun su.

Kara karanta wannan

Ba mu bada sarauta haka kawai: Sarkin Daura yayinda yaiwa Amaechi 'Dan Amanar Daura'

Jephthah Robert Yekorogha
Da Dumi-Dumi: Ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa da yan bindiga suka sace ya kubuta Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Hadimin ƙanin wanda ya kuɓuta, Azibaola Robert, shi ne ya tabbatar da lamarin a wani gajeren sako da ya fitar ranar Litinin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Muna miƙa dukkan godiya ga Allah bisa dawowar ɗan uwan mu, Jephthah Robert Yekorogha, daga sansanin masu garkuwa da mutane cikin ƙoshin lafiya."

Shin an biya kuɗin fansa?

Har yanzun babu cikakken bayani kan ko an biya kuɗin fansa, domin a sanarwan da iyalan suka fitar ba su yi bayani kan abin da ya shafi fansa ba.

Idan baku manta ba, iyalan ɗan uwan Jonathan da aka sace sun yi kira ga masu garkuwa su sako ɗan uwansu ba tare da wani sharaɗi ba kuma ba tare da sun illata shi ba.

Ɗan uwan mutumin, Mista Roberts, ya tabbatar da cewa jami'an tsaro sun maida hankali matuƙa kan kokarin ceto ɗan uwansu, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Tinubu karamin kwaro ne ba zai iya dakatar da ni ba, Dan takara a 2023

Ya kuma miƙa godiyarsa ga kwamishinan yan sanda na jihar Bayelsa da kuma Darakatan jami'an tsaro na farin kaya DSS bisa sadaukarwar da suka yi kan lamarin.

A wani labarin na daban kuma Fusatattun Mutanen gari sun hallaka tawagar yan fashi da suka kai hari

Mutanen gari sun samu nasarar kama wasu yan fashi da makami da suka addabi yankin su, kuma ba su yi wata-wata ba wajen aika su lahira.

Wani shaida ya bayyana cewa an kama mutum biyu daga cikin yan fashin yayin da suka shiga wani garejin gyaran mota a Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262