'Yancin mata ne: Gwamnatin Buhari ta magantu kan batun hana sanya Hijabi a makarantun Kwara
- Dokar Najeriya ta ba mata musulmi damar sanya Hijabi daidai da koyarwar addininsu, a cewar gwamnatin tarayya
- Adamu Adamu, ministan ilimi ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi 6 ga watan Fabrairu a babban masallacin kasa dake Abuja
- Takaddamar sanya Hijabi a Najeriya ya haifar da zazzafar muhawara a wasu sassan kasar, lamarin da ke kara kamari
FCT, Abuja - Ministan ilimi, Adamu Adamu, ya mayar da martani kan cece-kucen da ake tafkawa a baya-bayan nan kan yadda ake tauye hakkin mata musulmi da ke sanya hijabi a wasu sassan kasar.
Adamu ya bayyana cewa, kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba wa mata musulmi cikakken daman sanya Hijabi daidai da koyarwar addininsu, inji rahoton Daily Trust.
Ya bayyana hakan ne a wajen taron jama’a da kungiyar hadin kan mata musulmi ta Najeriya ta shirya a wani bangare na gudanar da bikin ranar Hijabi ta duniya na bana a ranar Lahadi 6 ga watan Fabrairu a babban masallacin kasa dake Abuja.
Ministan wanda ya samu wakilcin Hajiya Sidikat Shomope ta sashin wayar da kan jama’a na hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa (UBEC) ta yi nuni da cewa, an ba wa ‘yan kasa damar gudanar da addininsu matukar ba zai haifar da matsala ga sauran jama’a ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Adamu ya koka kan yadda ake ta rikice-rikice kan sanya hijabi a kasar nan a matakin makarantu da kuma fadace-fadacen da hakan ya haifar.
Ministan ya ce:
"Sanya hijabi ga mata musulmi Sunnah ce kamar yadda ya zo a cikin Alkur'ani (Q33:V59).
Da yake karin haske, ministan ya ce akwai dimbin riba da Najeriya za ta iya samu ta hanyar tattaunawa kan batutuwan da suka shafi addini maimakon tayar da hankali akai.
A kare mata masu hijabi daga cin zarafin masu suka
A wani rahoto da jaridar Nigerian Tribune ta fitar, kungiyar hadin kan mata musulmi ta Najeriya ta yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su kare mata masu hijabi daga cin zarafi da cin mutuncin wasu daidaiku.
Matan musulmi daga kungiyoyin Musulunci daban-daban sun yi wannan kiran na gaggawa da nufin kare martaba da mutuncin mata.
Hajiya Azeeza Jibrin, ‘yar kungiyar kare 'yan mata musulmi, da take jawabi a wajen bikin ranar Hijabi ta duniya ta bana, ta bayyana cewa hijabi ya kasance rigar mutunci da daraja ga diya mace.
A wani labarin daban, an hana daliban makarantar sakandaren Igboye dake garin Epe, jihar Legas biyu zana jarabawa saboda suna sanye da Hijabi.
Hakazalika an hanasu shiga makaranta makon da ya gabata yayinda ake shirin jarabawar.
Mahaifin daliban ya ziyarci makarantar inda ya nunawa Shugaban makarantar Mrs Odushoga hukuncin kotu da aka halaltawa dalibai sanya kayan addininsu.
Amma Shugabar makarantar ta lashi takobin cewa ba za'a barsu su zana jarabawa ba sa sun cire Hijabi, Kungiyar kare hakkin masu sanya Hijabi watau Hijab Right Advocacy Initiative ta bayyana a jawabi.
Asali: Legit.ng