Sarkin Daura: Ba mu bada sarauta don kuɗi, Amaechi ya cancanci naɗin da aka masa

Sarkin Daura: Ba mu bada sarauta don kuɗi, Amaechi ya cancanci naɗin da aka masa

  • Alhaji Umar Farouq, Mai martaba Sarkin Daura ya bayyana cewa masarautarsa ba ta raba sarauta hakan nan ba tare da mutane sun cancani sarautar ba
  • A ranar Asabar ne masarautar ta Daura ta karrama Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, da sarautar 'Dan Amanar Daura' saboda gudunmawar da ya bawa Katsina da Najeriya
  • Sarkin na Daura ya mika godiya a musamman ga gwamnatin tarayya, Sarkin Legas, sauran sarakunan gargagiya da malaman addini bisa goyon bayan masarautar Daura

Daura, Katsina - Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouq, ya ce Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya cancani sarautar da masarautar Daura ta ba shi.

Farouq ya yi wannan jawabin ne a ranar Asabar yayin nadin sarautar da aka yi a Daura, Jihar Katsina, rahoton The Cable.

An karrama Amaechi ne da sarautar 'Dan Amanar Daura' yayin bikin nadin da manyan mutane da dama suka hallarta.

Kara karanta wannan

Sarkin Daura: Amaechi ya cancanci sarauta a masarautar mu

Sarkin Daura: Ba mu bada sarauta don kuɗi, Amaechi ya cancanci naɗin da aka masa
Ba mu bada sarauta saboda kudi, Amaechi ya cancanta ne, Sarkin Daura. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Masarautar ta Daura ta ce an yi masa nadin ne saboda gudunmawa da dama da Ministan na Sufuri ya bada a bangaren sufuri a Najeriya.

Ba mu bada saura don kudi, sai wanda ya cancanta, Sarkin Daura

Farouq ya ce masarautar ba ta bada sarauta sai ga wadanda suka cancanta kuma ba ta bada sarauta saboda kudi.

Ya ce:

"Mun gode wa Allah mai girma, dukkan godiya sun tabbata ga Allah da ya bamu tsawon kwana muka ga wannan taron mai muhimmanci inda Masarautar Daura za ta nada sarauta ga ministan sufuri, Rotimi Amaechi.
"Ina godiya ga gwamnatin tarayya da masu sarautan gargajiya da shugabannin addini ciki har da Sarkin Legas bisa goyon bayan masarautar Daura.
"Magana ta gaskiya, Masarautar Daura ba ta bada sarauta haka nan sai dai ga wadanda suka cancanta kamar Amaechi."

Kara karanta wannan

Harin Boko Haram a Buratai: Shugaban Sojoji ya ziyarci Borno, ya tattauna da Sojoji

A cewar masarautar, sarautar da aka bawa Amaechi tukwici ne bisa karamcin da ya yi wa Katsina da arewa baki daya ta hanyar ayyuka da dama.

Sarkin Daura: Mun ba Yusuf Buhari sarauta ne don kada ya riƙa gararamba a Abuja bayan Buhari ya sauka mulki

A wani labarin, Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk, ya yi magana kan dalili da yasa aka nada Yusuf, dan Shugaba Muhammadu Buhari sarauta a Daura, rahoton Daily Trust.

Yusuf, wanda shine da namiji tilo na Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Asabar, aka nada shi sarautar Talban Daura kuma Hakimin Kwasarawa.

Da ya ke jawabi a fadarsa yayin bikin nadin sarautar sabbin hakimai hudu, a ranar Alhamis, sarkin ya ce nadin zai hana Talban yawo zuwa Abuja da Yola, garin mahaifiyarsa, bayan wa'adin mulkin Buhari ta kare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164