Rashin tsaro: Gwamnatin Borno ta bude titin iyakar Maiduguri–Dikwa–Gamboru/Ngala
- Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya bude titin iyakar Maiduguri–Dikwa–Gamboru/Ngala
- Gwamnan tare da rundunar sojojin Najeriya ne suka taru tare da bude titin wanda yayi shekaru masu yawa a rufe
- Mazauna yankin sun dinga farin ciki, murna da annashuwa kan bude titin inda suka ce hakan zai habaka tattalin arzikin yankin
Borno - Gwamnatin jihar Borno da rundunar sojin Najeriya a ranar Juma'a, suka sake bude titin Maiduguri - Dikwa - Gamborun Ngala domin kaiwa da kawowa, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.
Idan an tuna, an datse kaiwa da kawowa a titin iyakar mai tsawon kilomita 138 wanda ya hada Najeriya zuwa Kamaru da Jamhuriyar Chadi, saboda matsalar rashin tsaro.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, yayin jawabi a bikin bude titin a Maiduguri, Gwamna Babagana Zulum ya ce masu ababen hawa za su iya bin titin daga karfe 8:00 na safe zuwa karfe 2:00 na rana.
Zulum ya ce masu ababen hawa ba su bukatar daukar jami'an tsaron da za su yi musu rakiya daga Maiduguri zuwa Dikwa, jami'an tsaron hadin gwuiwa tare da mafarauta za su dinga musu rakiya na sauran tafiyar kimanin kilomita 60 daga Dikwa zuwa Gamborun Ngala.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bukaci masu ababen hawa su kiyaye dukkan dokokin da hukumomi suka gindaya musu yayin bin titin saboda tsare kawunan su da saukin kaiwa da kawowa.
A jawabin sa, kwamandar rundunar tsaron hadin gwuiwa, Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Christopher Musa, ya yi godiya ga Gwamnatin jihar Borno na tabbataccen karfafawan ta ga rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaron jihar.
"Muna karfafaku ne ba don ku zauna ba, muna baku tabbacin hadin kanmu da karfafawar mu a dukkan komai na tabbatar da Borno da arewa maso gabas baki daya, sun samu zaman lafiya mai dorewa," a cewar Musa.
Masu ababen hawa da matafiya a muryoyi daban-daban suke annashuwa da farin cikin cigaban, inda suka ce zai habaka tattalin arzirki ta fannin kasuwanci.
"Daga Maiduguri zuwa Gamborun Ngala nisan awa biyu ne kacal a mota, amma saboda matsalar rashin tsaro, muna daukar kusan kwana hudu kafin mu isa. Mun sha wahala matuka na tsawon shekaru.
"Yanzu da akwai damar kai-komo, babu abunda za mu ce sai dai mu godewa Ubangiji, muna godiya ga gwamna Zulum da rundunar sojin Najeriya," a cewar wani dan kasuwa, Idris Habib.
NAN ta ruwaito bikin bude titunan yayinda aka gabatar da motocin sintiri guda 10 ga sojoji, inda kungiyar mafarauta da rundunar hadin gwuiwan suke da motoci hudu kowannen su.
Zulum ya sake bude titin Bama zuwa Banki, shekara 9 bayan rufe shi
A wani labari na daban, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya sake bude titin Bama zuwa Banki mai nisan kilomita 76 domin farfado da lamurran kasuwanci tsakanin Najeriya da kasashe masu makwabtaka irinsu Kamaru da Chadi.
An rufe titin a shekarar 2012 sakamakon hauhawar al'amuran 'yan ta'addan Boko Haram.
Daily Nigerian ta wallafa cewa, a yayin jawabin bikin budewar a ranar Laraba a Bama, Zulum ya ce babu wani cigaba da za a samu wurin farfado da yankin ba tare da an dawo da lamurran kasuwanci ba.
Asali: Legit.ng