Layin dogon Kaduna-Kano: Da yiwuwan mu gaza kammalawa saboda rashin kudi, Amaechi

Layin dogon Kaduna-Kano: Da yiwuwan mu gaza kammalawa saboda rashin kudi, Amaechi

  • Ministan Sufuri ya bayyana cewa da yiwuwan su gaza kammala layin dogon Kaduna zuwa Kano kan lokaci kamar yadda akayi alkawari
  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kasar Sin ta daina bata bashin kudi don cigaba da wasu ayyuka
  • Wannan shine layin dogon na hudu da Gwamnatin Buhari ke kokarin ginawa

Jihar Kano - Ministan Sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi, ya yi gargadin cewa rashin kudi na iya zama cikas ga kammala ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano.

Ministan ya bayyana cewa yanzu haka Gwamnatin tarayya na neman kudi daga wurare daban-daban don kammala aikin.

Ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a Kano yayin ziyarar ganin ido da ya kai, rahoton TheNation.

Yace:

"Ban taba cewa bamu fuskantar kalubalen kudi ba, kuma saboda matsalar tattalin arziki ne. Yan kasar Sin sun daina bamu kudi yadda suka saba, har yanzu bamu kammala tattaunawa kan bashin wannan aiki ba."

Kara karanta wannan

Boka da magani: Yadda wata bokanya ke samun N1.8m a rana, ta mallaki makeken gida

"Saboda haka daga cikin kasafin kudi muke wannan aiki, shiyasa na fara shakkan ranar kammalawa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amaechi
Layin dogon Kaduna-Kano: Da yiwuwan mu gaza kammalawa saboda rashin kudi, Amaechi
Asali: Original

Nan da Disamba 2022 za'a kammala layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

A baya, Ministan Sufurin ya bayyana cewa nan da karshen 2022 za'a fara amfani da layin dogon Kano zuwa Kaduna.

Amaechi ya kara da cewa Gwamnatin tarayya kawo yanzu ta zuba $400million wannan aiki kuma za'a kammala a kaddamar kafin wa'adin Shugaba Buhari ya kare a ofis.

Ya kara da cewa yan majalisar zartaswa sun sauya tsarin da aka yi na kashe $1.2billion kan aikin daga farko har karshe.

Kasar Sin ta hana mu bashi, yanzu Turai zamu je nema

Kwanaki biyu da suka gabata, Amaechi, ya bayyana cewa dalilin da yasa aka gaza kammala wasu ayyukan layin dogo rashin kudi ne daga wajen gwamnatin kasar Sin.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Sule Lamido ya ce Tambuwal ne ya fi dacewa ya gaji Buhari, ya fadi dalili

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fara yunkurin neman yadda zata samu bashi daga wajen kasashen Turai tunda kasar Sin ta rike kudinta.

Ya bayyana cewa idan aka samu nasarar samun kudi daga wajen Turai, za'a kammala ayyukan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng