Ci gaba da shari'ar Abduljabbar: Kotu ta bukaci shaidan gwamnati ya sake bayyana
- A ci gaba da shari'ar Abduljabbar da gwamnatin Kano, an sake zama a kotu domin jin bangarorin gwamnati da na Abduljabbar
- Lauyoyin Abduljabbar sun bukaci kotu ta sake gayyato shaidan da lauyoyin gwamnati suka gabatar tun farkon shari'ar
- Alkali ya amince duk inkarin hakan daga tsagin gwamnati, yanzu an dage shari'ar zuwa 17 ga wannan watan ta Fabrairu
Jihar Kano - Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu karkashin jagorancin Ibrahim Sarki Yola, ta umarci shaidan mai gabatar da kara na farko da ya gurfana a gabanta a ranar 17 ga watan Fabrairun 2022 dangane da shari’ar Abduljabbar Nasiru Kabara.
Ana zargin Abduljabbar Kabara da batanci ga Annabi da kuma tunzura jama'a cikin karatukansa, Daily Trust ta ruwaito.
Lauyan Abduljabbar, karkashin jagorancin Ambali Obomeileh Muhammad, SAN, ya bukaci a dawo da shaidan mai gabatar da kara na farko da ya sake gurfana gaban kotu domin yi masa tambayoyi.
Lauyan mai gabatar da kara, karkashin jagorancin Barista Sa’idu Suraj, SAN, ya ki amincewa da bukatar da aka gabatar, inda ya bukaci kotun da ta janye bukatar.
A cewarsa:
“An ba su isasshen lokaci, akalla makonni 4 don shiryawa.
“Za mu ji batun kariya kuma sun kawo wannan a yanzu, bata lokaci ne kawai."
Sai dai alkali ya amince da bukatar lauyoyin Abduljabbar, sannan ya umarci shaidan mai gabatar da kara na farko da ya sake bayyana a gaban kotun.
An dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan Fabrairu.
Idan baku manta ba, ana tuhumar Abduljabbar ne bisa wasu tuhume-tuhume guda hudu ciki har da zagi da kuma yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Shari'ar Abduljabbar da ta Dan Sarauniya
Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Muazu Magaji, wanda aka fi sani da Dan Sarauniya, zai kara kwana daya a gidan gyaran hali.
Daily Trust ta rahoto cewa hakan ta faru ne saboda ranar cigaba da shari'arsa ya ci karo da na Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, wanda ke gaban kotu kan zargin batanci ga Annabi (SAW).
A wata takarda, kwamishinan yan sanda na jihar Kano ya shaida wa alkalin kotun Majistire mai lamba 58 dake Nomansland, matsalar da aka samu da shari'ar Magaji.
"Alkalin kotun Majistire a Nomansland ya umarce ni na sanar da kai cewa kasancewar za'a cigaba da zaman shari'ar Sheikh Abduljabbar ranar 3 ga wata, wanda ya hadu da shari'ar Magaji, wacce za'a yanke hukunci kan Beli.
"Saboda haka tun da jami'an tsaron ne za su kai Abduljabbar kotun musulunci dake K/Kudu, wannan Case na Dan Sarauniya an dage shi zuwa 4 ga watan Fabrairu, da misalin karfe 2:30 na rana."
A wani labarin daban, Barista Aisha Mahmoud, daraktar shigar da kara a jiya ta sanar da kotun majistare da ke tuhumar wasu mutane uku da suka kashe Hanifa Abubakar, cewa a dakatar da shari'ar bayan shigar da wata sabuwar kara a gaban wata babbar kotun Kano.
Jaridar This Day ta rahoto cewa, Aisha ta kara da cewa lauyan masu shigar da kara, ya shaida wa Alkalin kotun cewa:
“Mun shigar da karar ne, saboda laifin da ake zargin wadanda ake tuhumar sun aikata, wannan kotu ba ta da hurumin yin shari’ar."
Asali: Legit.ng