Labari mai dadi: CBN ya cire kudaden da ake cajin kwastomomi na ATM da sauran cajin banki
- Babban bankin Najeriya ya bayyana kudaden da suka dace ake cirewa a bankunan dangane da korafe-korafen da ‘yan Najeriya ke yi game da yadda ake zaftare kudadensu a bankuna
- CBN ya kuma sanar da rage farashin harkokin hada-hadar kudi ta intanet; daya daga cikin batutuwan da ake ta cece-kuce a tsakanin bankuna da kwastomomi
- Bankunan Najeriya sun samu makudan kudade daga hada-hadar kasuwanci da intanet da wayoyin hannu da suka kai sama da Naira biliyan 200 a 2021
FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi nazari kan kudaden da ake kashewa da kuma adadin kudaden da ake cirewa kwastomoni a harkokin bankuna a kasar.
CBN ya bayyana hakan ne a cikin wata sabuwar takardar da ya fitar mai taken ‘Guide to Charges by Banks Other Financial and non-Financial’ kamar yadda Daily Independent ta rahoto.
Babban bankin na CBN ya ce hakan zai shafi dukkan bankuna da kuma cibiyoyin hada-hadar kudade a duk fadin Najeriya.
Sanarwar ta bayyana cewa CBN ya rage wasu cajin da suka hada da na 'Standing Order Charge'; Kudin Gudanar da ATM; canjawa kudi wurin zama daga asusu zuwa wani asusun da tura kudi da yawa da dai sauransu.
A cikin sabuwar ka’idar, CBN ya ce kudaden da ake cirewa na 'Standing Order Charge' na banki zai kasance kyauta idan aka kwatanta da N300 a cikin ka’idar 2017.
Dangane da tura kudade tsakanin bankuna, CBN ya rage cajin kudi zuwa N50 a kowane ciniki idan aka kwatanta da N300 da aka bayyana a 2017, kamar yadda NAN ta bayyana.
Biyan Kudi (ciki har da biyan kudaden wutan lantarki da danginsu) za a iya ciniki akan iyakar N500 ga kowane hulda wanda mai aikawa zai biya, ragi daga N1,200 ko 0.75% na kudin da ake son biya.
Hakanan an sake duba tsarin tura kudi wato 'transfer' ta intanet zuwa N10 a kan N5000; N26 a N5001 zuwa N50,000 yayin da sama da N50,000 za a caji N50.
An rage farashin cire kudi daga mashunan ATM na wasu bankuna daga N65 zuwa N35 bayan cirewa na uku a cikin wata guda.
CBN ya kuma rage kudin biya na ATM daga N100 zuwa N50. An cire kudaden kula da katin zare kudi na ATM na N100 a wata a cikin sabuwar dokar.
Sabbin bayanai 4 game da Dangote da baku sani ba: Zai iya kashe N415m kullum na tsawon shekaru 40
A wani labarin, kamar yadda mujallar Forbes ta fitar a baya-bayan nan, karin 30% na farashin hannun jarin simintin Dangote wanda ya biyo bayan karuwar gine-ginen a Najeriya daga 'yan kasa da gwamnati ya ba da gudummawa ga karin dukiyarsa.
Legit.ng a bincikenta, ta kawo muku wasu sabbin abubuwa guda 4 masu ban sha'awa game da hamshakin attajirin wanda a halin yanzu dukiyarsa ta kai dala biliyan 13.9.
Karuwar arzikin da Dangote ya samu ya sa attajirin zai iya kashe dala miliyan 1 (N415m) a kullum nan da shekaru 40 masu zuwa.
Asali: Legit.ng