Sanatoci ga jami'an tsaro: Ya zama muku dole ku ceto mutum 38 da aka sace a Katsina
- Majalisar dattawa ta bukaci hukumomin tsaro da su shiga duk wasu mafakar masu garkuwa da mutane domin ceto mutanen da aka sace a Katsina
- A ranar Lahadin da ya gabata ne dai mahara suka kai farmaki garin Ruwan Godiya da ke karamar hukumar Faskari ta Katsina inda suka yi awon gaba da mutum 38
- Da yake jan hankalin majalisa kan lamarin, Sanata Bello Mandiya ya ce lamarin fashin daji da garkuwa da mutane na kara kamari a Katsina duk da kokarin gwamnati kan haka
Abuja - Majalisar dattawa a ranar Laraba, 2 ga watan Fabrairu, ta bukaci hukumomin tsaron kasar da su kakkabe dukkanin mabuyar masu garkuwa da mutane da nufin ceto mutane 38 da aka yi garkuwa da su a Katsina.
Hakan ya biyo bayan wani kudiri na Sanata Bello Mandiya wanda ya ja hankalin takwarorinsa zuwa ga hauhawan fashin daji da garkuwa da mutane a Katsina duk da kokarin gwamnati ta kawar da annobar ta hanyar kafa Operation Sharan Daji.
Ya ce an yi garkuwa da mutum 38 a ranar Lahadi da ta gabata lokacin da yan bindiga suka farmaki garin Ruwan Godiya a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, Daily Trust ta rahoto.
Dan majalisar ya bayyana cewa lamarin fashin daji da garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a Katsina. Ya kara da cewa ayyukan yan bindiga ya yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi, hanyar neman na abinci sannan ya daidaita garuruwa.
Ya nuna damuwa cewa kalubalen da lamarin tsaro ke ci gaba da fuskanta da hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa garuruwa da kauyuka a karamar hukumar Faskari sun jefa mutane cikin kangin rayuwa sannan ya sanya yankunan cikin barazana.
Mandiya ya yi gargadin cewa idan ba a dauki matakin gaggawa kan wannan annoba ba, abun zai shafi yalwar abinci tunda mafi yawan mutane a garuruwan da abin ya shafa manoma ne.
A hukuncinta, majalisar dattawan ta umurci jami’an tsaro da su kara zage damtse wajen ganin an ceto mutanen da aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya.
Haka kuma ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta tura isassun jami’an soji da jiragen yaki domin kamo ‘yan bindigar tare da dawo da zaman lafiya a yankunan, rahoton Punch.
'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda
A gefe guda, mun kawo a baya cewa jimillar mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.
Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.
Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.
Asali: Legit.ng