Makashin Hanifa Abubakar: Kotu ta dage zaman hukunta AbdulMalik Tanko
- Kotu dake sauraron karar makashin yar makaranta a Kano ta sake dage zaman da mako guda
- Kungiyoyin kare fararen hula irinsu kungiyar mata lauyoyi na daga cikin wadanda suka halarci zaman kotun na yau
- AbdulMalik ya bayyanawa jami'an yansanda cewa lallai shi ya kashe Hanifa amma bai yi mata gunduwa-gunduwa ba
Kotun majistaren dake zamanta ajihar Kano ta sake dage zaman sauraron karar kisan Hanifa Abubakar, 'yar shekara biyar da ake zargin shugaban makaranta ya hallaka kwanaki.
Kotun ta bada umurnin cigaba da tsare AbdulMalik Tanko a gidan yari na tsawon mako guda zuwa ranar 9 ga Febrairu, 2022, rahoton sashen Hausa na BBC.
Rahoton ya kara da cewa Lauyoyin gwamnati karkashin jagorancin Barista Aisha Mahmud ne suka nemi a sake tsare mutane hudun da ake zargi har zuwa nan da mako guda.
Lauyoyin sun bukaci hakan ne don samun damar gurfanar da su a wata babbar kotu da ke da hurumin sauararen kara saboda kotun majistare ba da ta hurumi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda Shugaban makaranta ya sace dalibarsa kuma ya kasheta a jihar Kano
Mammalakin makarantar Noble Kids School dake jihar Kano ya shiga komar yan sanda kan laifin garkuwa da kashe dalibar makarantarsa, Hanifa Abubakar yar shekara biyar.
Yan'uwanta sun bayyana cewa yana daya daga cikin wadanda suka je gidan iyayenta jajanta musu lokacin da aka sace ta.
Kakakin hukumar yan sanda a Kano, SP Kiyawa yace an damke Malamin, Abdulmalik Tanko, wanda yayi garkuwa da ita.
Yace bayan dogon bincike da bibiya, jami'an DSS sun damke Abdulmalik Mohammed Tanko da Hashim Isyaku, yan unguwar Tudun Murtala Quarters, karamar hukumar Nassarawa.
Yayin bincike, AbdulMalik ya amsa cewa Hanifa dalibarsa ce a makaranta kuma ya saceta kuma ya kasheta bayan da ta ga fuskarsa.
Tuni matasa suka dira makarantar inda suka banka mata wuta.
Asali: Legit.ng