Kaduna: 'Yan ta'adda sun bindige tsohon dan takarar ciyaman da abokinsa
- Miyagun 'yan bindiga sun harbe tsohon dan takarar shugaban karamar hukuma a zaben jihar Kaduna da ya gabata
- Steven Inuwa ya sheka lahira yayin da 'yan bindiga suka tsare su da abokinsa a babban birnin tarayya da ke Abuja ranar Lahadi
- Miyagun 'yan bindigan sun bude wa abokan biyu wuta inda Agatha ya rasu a take, yayin da Inuwa ya rasu a wani asibiti da ke Bwari
Kaduna - 'Yan bindiga sun harbe tsohon dan takarar shugaban karamar hukuma a zaben kananan hukumomi a jihar Kaduna, Steven Inuwa, a ranar Lahadi da ta gabata a Abuja.
Inuwa wanda ya yi takara karkashin jam'iyyar Peoples’ Democratic Party (PDP) ya rasu a asibitin Bwari, Daily Trust ta ruwaito.
Miyagun 'yan ta'addan sun hada da Ernest Agatha sun kashe shi bayan sun harba bindiga kan motarsa da ya ke tukawa wurin yankin Zuma a gefen birnin Bwari, Daily Trust ta ruwaito.
Wani makusancin mamacin mai suna John Alpha, yayin zantawa da City News, ya ce Agatha ya na tuka motarsa ne inda ya rasu a take, yayin da aka garzaya da dan siyasan asibitin Bwari inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya, DSP Josephine Adah, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya kara da cewa ana cigaba da bincike.
Tashin hankali: Masu garkuwa da mutane sun 'kwace' iyakokin jihohi 2 a Najeriya
A wani labari na daban, masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga sun kwace titin da ke tsakanin Uturu na karamar hukumar Isiukwiato da ke jihar Abia zuwa karamar hukumar Okigwe na jihar Imo.
A binciken da Daily Trust tayi, ya bayyana yadda yan ta'addan suke cin karen su ba babbaka kan titin, a kowacce rana ko dai su kashe ko kuma su yi garkuwa da mutane.
Tsakanin Disamba zuwa Janairu, an yi garkuwa da kimanin mutane 25, inda aka halaka mutane biyar, duk da akwai matsayar jami'an tsaro guda biyu a kan titin.
Mazauna yankin Uturu sun nuna damuwar su matuka game da yadda ake kashe-kashe da garkuwa da mutane a kan titin Okigwe zuwa Uturu.
Asali: Legit.ng