Katsina: Jiragen NAF sun yi lugude a sansanin Gwaska, sun sheke 'yan ta'adda 43
- Jiragen saman dakarun sojin Najeriya sun yi wa sansanonin 'yan ta'adda a kananan hukumomin Safana da Dan Musa a jihar Katsina ruwan wuta
- An ga gawawwaki 43 na 'yan ta'adda da ke biyayya ga shugabannin 'yan bindiga Gwaska da Alhaji Abdulkarimu birjik
- Sojojin sun yi ruwan wutan ne a yankin tsaunika da ke kauyen Ilela, inda 'yan ta'addan ke bajewa bayan sun kai wa jama'a farmaki
Katsina - Luguden wuta ta jiragen sama da ake cigaba da yi wa sansanonin 'yan ta'addan a arewa maso yammaci ya yi ajalin manyan shugabannin 'yan ta'adda da mukarrabansu a jihar Katsina.
PRNigeria ta tattaro cewa, luguden da jirgin NAF ya yi a yankin Ilela na jihar Katsina a ranar Lahadi, ya janyo ajalin 'yan ta'adda masu tarin yawa na sansanonin Gwaska Dankarami da Alhaji Abdulkarami, fitattun shugabannin 'yan bindiga 2.
An gano cewa, 'yan ta'addan da aka halaka su ke da alhakin kai jerin hare-hare a yankunan kananan hukumomin Safana da Dan Musa a jihar Katsina.
An aiwatar da luguden ne ta jiragen NAF a kan tsaunikan yankin Ilela, inda 'yan ta'addan ke boyewa suna shan iska bayan kai farmaki tare da halaka jama'a.
Wata majiyar sirri ta tabbatar da nasarar da aka samu na kashe 'yan ta'addan bayan luguden wutar.
"Bayan samun rahoton farmakin da 'yan ta'addan ke kaiwa kauyukan karamar hukumar Safana, balle kauyen Ilela inda suka kashe mutane 12 a kwanan nan tare da fatattakar wasu, dakarun sama na Operation Hadarin Daji sun duba wurin tare da tsara yadda za su magance matsalar.
“Bayanin da ISR suka samu ya nuna cewa, 'yan ta'addan suna lamurran rayuwarsu a tsaunikan da ke da nisan kilomita 1.5 daga kudu maso yammacin Ilela da kudancin kauyen Rubu. An hango 'yan ta'addan a kan babura 19 bayan sun kai farmaki kauyikan.
Kamar yadda majiya daga yankin ta sanar bayan kammala ayyukan sojojin, PRNigeria ta tattaro cewa an halaka 'yan ta'adda masu tarin yawa.
"Jiragen saman sun ragargaji 'yan ta'addan da ke kan babura da bama-bamai a yankin tsaunikan. A kalla gawawwakin 'yan ta'adda 43 aka samu har da ta Alhaji Shingy, dan uwan marigayin shugaban 'yan bindiga Auta.
"Mayaka masu tarin yawa da ke karkashin Dankarami da Abdulkarimu sun sheka lahira, kayan aikin su da baburan su duka sun kone," majiyar tace.
Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto
A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan Najeriya ta halaka wasu mutum 23 da ake zargin 'yan ta'adda ne, inda suka sake kama yan bindiga guda 37 a kananan hukumomi uku da ke jihar Sokoto.
Yayin zantawa da manema labarai ranar Litinin a Sakkwoto, mataimakin Sifeta Janar, Ahmad Zaki, ya bayyana yadda aka kama wadanda ake zargin da bindiga kirar AK-47 guda 32, makamai masu linzami guda 2, harsasai sama da carbi 1,000 da mugayen makamai.
Ya ce an gano hakan ne lokacin da 'yan sanda suke gudanar da aiki na musamman domin yaki da ta'addanci wanda su ka yi wa lakabi da "Operation Sahara Storm".
Asali: Legit.ng