'Yan sanda sun kusa kwamushe Malamin Addini saboda hangen faduwar Tinubu a 2023, ya yi martani
- 'Yan sanda sun gayyaci wani fasto da ya yi hasashen faduwar Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023 domin ya amsa tambayoyi
- Sai dai faston, Adelana Solomon, ya ce ko a kwalar rigarsa domin bai girgiza da gayyatan ba
- Malamin ya ce idan har Tinubu ya hau kujerar toh ba zai shekara hudu ba zai mutu
Lagos - Wani mai wa'azi a kafar sadarwa ta Instagram, Adelana Solomon, wanda aka fi sani da Oba Solomon, ya yi martani ga wata gayyata da yan sanda suka yi masa inda suka bukaci ya ziyarci hedkwatar Zone 2 a Onikan, Lagas a ranar Laraba.
Punch ta rahoto cewa a wani bidiyon kai tsaye a Instagram a ranar Talata, 1 ga watan Fabrairu, Solomon, wanda ke da mabiya sama da 213,000, ya fada ma masoyansa cewa kada su ji tsoron komai.
Ya ce:
“Babu abun da zai faru, Ina nan a gida, babu abun da zai faru.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Solomon, wanda yayi ikirarin cewa shi fasto ne a cocin Cherubim and Seraphim Church of Zion, Oke Igbala, a yankin Lekki da ke jihar Lagas, ya yi kakkausar suka ga jam’iyyar APC da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan rashin shugabanci mai kyau a Instagram.
Ya kuma yi hasashen cewa jigon APC, Bola Tinubu, wanda ya ayyana aniyarsa ta takara don ya gaji Buhari, ba zai zama shugaban kasa ba a 2023.
Ya ce:
“Idan ni bawan Allah ne, Tinubu ba zai zama Shugaban kasa ba. Idan ka zama shugaban kasa, Za ka mutu kafin shekaru hudu.”
An tattaro cewa rundunar yan sandan Najeriya ta gayyaci faston mazaunin Lekki domin amsa tambayoyi.
A wata wasika mai kwanan wata 27 ga watan Janairu, 2022, ana sa ran Solomon ya kasance a ofishin yan sandan Zone 2, Onikan Lagas a ranar Laraba domin yi masa tambayoyi, rahoton Sahara Reporters.
A cewar wasikar:
“Ofishin na binciken wata kara da aka kai gaban mataimakin sufeto janar na yan sanda, reshen Zone 2, Onikan Lagas.
“Domin yin bincike, ana neman ka zo ofishin da ke kula da korafe-korafe, CSP Olukode Taofiki a ranar 2 ga watan Fabrairu, 2022 da karfe 10:00.”
Da aka tuntube shi a ranar Talata, Taofiki ya tabbatar da wasikar, jaridar Punch ta rahoto.
Ya ce:
“Da gaske ne, akwai korafi a kansa.”
Sai dai bai bayyana wani irin korafi bane aka shigar a kansa din.
Takara a 2023: Kungiyar CAN ta yi watsi da Yahaya Bello, ta yi karin bayani a kansa
A wani labarin kuma, kungiyar Kiristocin Najeriya a jihohin arewa 19 da Abuja ta yi watsi da rahotannin cewa ta marawa takarar shugaban kasa na Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi baya a zaben 2023.
CAN ta bayyana hakan ne a wata sanarwar da ta fitar bayan wani gagarumin taro da ta gudanar a otal din Excel da ke Abuja, PM News ta rahoto.
2023: Malaman addinin Musulunci da Kirista fiye 1,000 sun yi taron yi wa gwamnan APC addu’o’in samun nasara
Jami'in hulda da jama'a na kungiyar CAN a jihohin arewa da Abuja, Chaplain Jechonia Gilbert, ya ce kungiyar bata taba tsayar da wani mutum don darewa wata kujerar shugabanci a tarihin zabe a Najeriya kuma ba za ta aikata hakan ba a zaben 2023.
Asali: Legit.ng