Katsina: An kama boka da ke yi wa 'yan bindiga asiri da addu'oin samun sa'a
- Yan sanda a Jihar Katsina sun yi nasarar kama wani boka, Abdullahi Bello mai shekaru 50 dan asalin Jamhuriyar Nijar
- An kama Bello ne bayan wasu yan bindiga da suka shiga hannun yan sanda sun ce shi ke musu asiri da addu'o'i na samun sa'a idan za su hari
- Yan sanda sun kama bokan, Abdullahi Bello tare da babura biyu, wayoyin salula guda takwas da layyu da guru masu yawa
Katsina - Rundunar yan sandan Jihar Katsina ta yi nasarar kama wani Abdullahi Bello, dan shekara 50, wani boka da ke yi wa yan bindiga asiri da addu'o'i a Katsina da kewaye domin su rika kai wa mutanen jihar hare-hare.
Jaridar Vanguard ta ruwaito yan sandan sun ce sun kwato babura biyu, wayoyin salula takwas da layyu da dama a hannun bokan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kakakin yan sandan jihar, SP Isah Gambo ya yi holen wadanda ake zargin, a hedkwatan yan sandan a ranar Litinin tare da wasu yan ta'adda hudu da ake zarginsu da hannu cikin sace Ammar.
Yan bindigan da yan sanda suka kama ne suka tona asirin bokan
Wasu gungun yan bindiga ne suka tona asirin bokan wanda dan asalin kauyen Kandamau ne a Jamhuriyar Nijar da ake bincike kan sace wani Ammar Abdulkadir a Katsina a ranar 12 ga watan Janairun 2022.
Yan bindigan, yayin da suke amsa laifinsu sun ce sun hada baki da wani Ibrahim da aka fi sani da 'Namadi' da wasu yan ta'addan da ke dajin Dumburum domin kai hare-haren.
A cewar kakakin yan sandan SP Sambo:
"Shugaban tawagar masu yaki da garkuwa da mutane, CSP Alphonse Andrew ya yi bincike, hakan ya yi sanadin kama wanda suka kitsa garkuwar da wasu garkuwan daban da sace shanu da aka yi a yankin."
"Yan ta'addan da aka kama sun hada da Yusuf Usman 27, mazaunin Bayan Gidan Lema Jibrin, Katsina, Kabir Bello 20, Yammawa Quarters Katsina, Sani Musa 31, na Tudun Baras Quarters Katsina, Salisu Ya’u, alias “Mai Rafanai” 37, mazaunin kauyen Kwarare, Jibia.”
Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi
A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.
An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.
Yan sandan suna zarginsa da:
"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci".
Asali: Legit.ng