Bayan ayyana aniyar gaje kujerar Buhari, EFCC ta gurfanar da sanata bisa sace kudi

Bayan ayyana aniyar gaje kujerar Buhari, EFCC ta gurfanar da sanata bisa sace kudi

  • Hukumar EFCC ta gurfanar da sanata Rochas Okorocha bisa zargin sace kudaden gwamnati a wasu lokuta
  • An zargi Okorocha ne da hada baki da wasu 'yan APC da kuma wasu kamfanoni wurin aikata wannan laifi
  • Rahotannin da muke samu sun bayyana cewa, ana zargin Okorocha da cinye akalla Naira biliyan 2.9 na gwamnati

Hukumar EFCC ta gurfanar da sanata kuma tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha da zargin yashe kudaden gwamnati da suka kai N2.9bn.

An zarge shi da hada baki da wasu da suka hada da wani dan siyasan APC da wasu kamfanoni guda biyar a wannan wawura ta kudaden jama'a.

Bayan ayyana aniyar gaje kujerar Buhari, EFCC ta gurfanar da sanata bisa sace kudi
Bayan ayyana aniyar gaje kujerar Buhari, EFCC ta gurfanar da sanata bisa sace kudi | Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Takardun da Premium Times tace ta samo sun ce, hukumar ta EFCC ta shigar da kararraki 17 a ranar Litinin, a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Dangote, Lawan, Jiga-jigan siyasa sun halarci auren 'dan gidan IGP na yan sanda

Baya ga sanata Okorocha, sauran wadanda ake tuhumar sun hada da Anyim Nyerere Chinenye, Naphtali International Limited, Perfect Finish Multi Projects Limited, Consolid Projects Consulting Limited, Pramif International Limited, da Legend World Concepts Limited.

An dai shigar da karar ne a daidai lokacin da sanata Okorocha ke bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

EFCC ta damke tsohon gwamna, Rochas Okorocha, a Abuja

Rochas Okorocha, ya shiga hannun hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, jaridar Premium Times ta tabbatar.

Jami'an hukumar EFCC sun kama Okorocha wurin karfe 4 na yammacin Talata a ofishinsa dake Abuja, majiya ta tabbatar.

Majiyar da ta tabbatar, ta ce hukumar ta dinga tura gayyata ga tsohon gwamnan zuwa ofishinta dake Abuja saboda harkallar wasu kudade amma ya ki zuwa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Dan majalisar dokokin jihar Zamfara, Ibrahim Na-idda, ya mutu

Okorocha, wanda yanzu sanata ne, ya ki zuwa gayyatar da aka yi masa, lamarin da ya fusata hukumar EFCC din kuma suka san hanyar kama shi.

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya yi alkawarin gina jami’ar addinin musulunci a mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar Premium Times ta ce Sanata Rochas Okorocha ya bayyana cewa gidauniyar nan ta sa, Rochas Okorocha Foundation, za ta yi wannan babban aikin.

Jigo kuma Sanatan na jam’iyyar APC zai kafa wannan jami’a ne a garin Daura, Arewacin jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.