Tafiya a mota: Gwamna ya makale a hanyar Kaduna, jirgi ya dauke shi cikin gaggawa

Tafiya a mota: Gwamna ya makale a hanyar Kaduna, jirgi ya dauke shi cikin gaggawa

  • Gwamnan jihar Neja ya makale a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja yayin da yake tafiya a mota da tawagarsa
  • Wani jirgi mai saukar ungulu ya sauko nan take domin tabbatar da an dauki gwamnan zuwa inda zai je cikin koshin lafiya
  • An ce cunkoso ne ya sa gwamnan da wasu matafiya samun matsala a hanyar da ke da yawan matsalolin rashin tsaro

Jihar Kaduna - Wani jirgin sama mai saukar ungulu ya dauki Gwamna Abubakar Sani Bello na Neja a lokacin da ayarinsa ke makale a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ranar Lahadi, 31 ga watan Janairu, New Telegraph ta ruwaito.

Gwamnan dai da alama yana kan hanyarsa ta dawowa ne daga ziyarar ta'aziyyar Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamali, bisa rasuwar Hakimin Hammanu Dauda, ​​a lokacin da cunkoso ya rutsa da shi.

Kara karanta wannan

Hotunan 'ya'yan jam'iyyar APC reshen UK yayin da suka ziyarci Tinubu a Ingila

Gwamnan jihar Neja
Gwamnan Neja ya makale a hanyar Abuja, an turo jirgi ya dauke shi cikin gaggawa | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Wani jirgin sama mai saukar ungulu ne ya dauki Abubakar daga kan hanyar yayin da sauran matafiya suka makale a kan babbar hanyar, kamar yadda ARISE News ta ruwaito a ranar Litinin.

Lokacin da manema labarai suka tuntubi babbar sakatariyar yada labaran gwamnan Mary Noel-Berje domin jin ta bakinta, ta yi alkawarin ba da bayani ta SMS, wanda har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba ta yi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Titin Abuja zuwa Kaduna wanda ya zama mafakar ‘yan fashi da makami, na daya daga cikin hanyoyin da matafiya ke bi daga yankin Arewacin kasar nan zuwa kudanci.

Da yake magana kan musabbabin cunkoson ababen hawan, kakakin hukumar FRSC Bisi Kazeem ya bayyana cewa lamarin ya kara kamari ne bayan wani hadarin mota da ya afku a kan babbar hanyar.

Ya ce an baza jami’an hukumar FRSC akan hanyar domin sanya ido da kuma sassauta matsalar cunkoson.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Gobara ta yi kaca-kaca da wani gidan mai mallakar ministan Buhari

Majalisar Wakilai ta Jihar Kaduna a watan Nuwamba 2021 ta nemi goyon bayan kawo karshen matsalar rashin tsaro a kan babbar hanyar.

Wani jirgin sama da ya dauko 'yan sanda ya yi hatsari a Bauchi

A labari mai kama da wanann, gidan talabijin na Channels ta ruwaito cewa, wani jirgin sama mai saukar ungulu na ‘yan sanda da ya taso daga Abuja ya yi hatsari a filin tashi da saukar jiragen sama na Bauchi, Hukumar Binciken Hatsari ta bayyana a ranar Alhamis.

Sai dai, ba a sami asarar rai ba, in ji rahoton na AIB.

A cewar sanarwar da The Nation tace ta samo:

“A ranar 26 ga Janairu, 2022, Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Najeriya (NAMA) ta sanar da Ofishin Binciken Hatsarin Hatsari, Najeriya game da wani hatsarin da ya rutsa da wani jirgin sama mai lamba Bell 429 mai lamba 5N-MDA mallakin rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF).

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano, Rimin-Gado, ya koma PDP

A wani labarin, daya daga cikin kamfanonin jiragen saman Najeriya, Arik Air da ya tashi daga Legas zuwa Asaba kana ya yi hatsari a wani yanki mai nisa a babban birnin jihar Delta da ke Kudu maso Kudu.

Rahotanni sun nuna cewa sama da fasinjoji 25 ne suka shiga jirgin da misalin karfe 6 na yamma a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya.

AIT ta ce ta yi kokarin tabbatar da labarin daga mahukuntan kamfanin amma hakan bai samu ba. Sai dai daya daga cikin jaruman fina-finan Nollywood, Uche Elendu, wacce tana daya daga cikin fasinjojin ta ce sun tsallake rijiya da baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.