Innalillahi: Gobara ta yi kaca-kaca da wani gidan mai mallakar ministan Buhari

Innalillahi: Gobara ta yi kaca-kaca da wani gidan mai mallakar ministan Buhari

  • Wani katafaren shahararren gidan mai a jihar Abia, mallakar daya daga cikin ministocin Buhari ya kone kurmus
  • Lamarin ya faru ne yayin da wata tankar mai ke sauke kaya a cikin gidan man, inda wutar ta yi barna mai yawa
  • Rahotannin da muke samu basu ba da labarin mutuwar wani ba, amma dai an ce gobarar ta kone abubuwa

Jihar Abia - Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, gobara ta lalata wani gidan mai na karamin ministan ma'adinai na Najeriya, Dr. Uche Ogah.

Gidan man mai suna Masters Energy yana kan titin Aba, titi mai yawan cunkoso a karamar hukumar Umuahia ta Arewa a jihar Abia.

Gobara ta ci gidan man minista
Innalillahi: Gobara ta yi kaca-kaca da wani gidan mai mallakar ministan Buhari | Hoto: infocus.com
Asali: UGC

Gobarar ta haifar da firgici a babbar hanyar, lamarin da ya sa aka karkatar da ababen hawa zuwa wasu hanyoyin daban, don dakile lalata wasu kadarori da ababen hawa da ke bin hanyar, kamar yadda Daily Sun ta rahoto.

Kara karanta wannan

Basarake da 'yan tawagarsa na asibiti rai a hannun Allah bayan harin da aka kai masa

Babu wanda ya mutu a gobarar da ta kama wata tankar mai da ke dauke mai a gidan man.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mukaddashin Kwanturolan hukumar kashe gobara ta Abia, Mista Arua Nnanna, a wata hira ta wayar tarho, ya ce tankar tana fitar da mai lita 43,000 a gidan mai a lokacin da wutar ta tashi.

Ya ce gobarar ta tashi ne sakamakon wani janareta da ake amfani da shi wajen sauke mai daga tankar.

A cewarsa:

“A bayanin da muka samu, janaretan da suka yi amfani da su wajen sauke mai daga tanka zuwa ma'ajiyar mai ne ya kama wuta.
“Ba su iya kashe wutar ba. An kira mu jami’an kashe gobara na gwamnatin tarayya da na jiha muka dauki matakin shawo kan gobarar.
“Wani bangare na gidan man ya kone, amma labari mai dadi shine babu wanda ya mutu. Mun kare kadarorin miliyoyin Nairori domin da ba mu zo ba, da barnar da za a yi a gidan da zai yi matukar yawa."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun koma soja bisa aikata 'fashi da makami' a Yobe

Ya kuma bukaci masu gidajen man da su tabbatar sun samar da na’urorin kashe gobara, ya kuma kara da cewa su kuma tabbatar da cewa sun gayyaci jami’an kashe gobara a duk lokacin da za su sauke man fetur a gidan man, domin gudun matsala.

Shugaban ma’aikatan gwamnan jihar, Mista Anthony Agbazuere, da sauran su, sun kasance a wajen domin tabbatar da ganin an kashe gobarar.

Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani katafaren gidan mai

A wani labarin, shahararren gidan man da ke garin Ibadan a jihar Oyo, SAO, dake unguwar Falana, Challenge, Ibadan, a ranar Talata da yamma ya kama da wuta, Tribune ta rahoto.

Gobarar wadda ta tashi da tsakar rana ta tashi ne da wata tanka da aka ajiye a harabar gidan man, lamarin da ya yi sanadiyar konewar sassan tashar da dama.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, an ga jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Oyo sun isa wurin da lamarin ya faru kuma a halin yanzu suna ta faman kashe gobarar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tankar man fetur ta fashe ta kama da wuta a tsakiyar gidan mai mallakin ministan Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.