Yadda muke amfani da keken adaidaita sahu wajen kwacen wayoyi a Kano, Wadanda ake zargi
- Jami'an yan sanda sun yi ram da masu yiwa fasinjoji kwacen wayoyi a adaidaita sahu a jihar Kano
- Rundunar ta kuma kama wasu barayin babur da yan daba a wurare daban-daban na jihar
- An yi nasarar kama matasan wadanda ke tsakanin shekaru 18 zuwa 20 bayan samun korafe-korafe daga mazauna jihar
Kano - Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama matasa 28 a wurare daban daban kan laifuka mabanbanta, inda wasu suka ce suna amfani da adaidaita sahu wajen yiwa fasinjoji kwacen wayoyinsu.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa rundunar ta kuma kama wasu kan satar babur da dabanci.

Source: UGC
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, yayin da yake gurfanar da wadanda ake zargin, ya ce an yi kamun ne bayan rundunar ta samu korafe-korafe daga mutane daban-daban.

Kara karanta wannan
Na sanar da Atiku cewa ya tsufa kuma gajiye ya ke, ba zai iya shugabanci ba, Gwamnan Bauchi
Kiyawa ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Mun samu yawan korafe-korafe a makon da ya gabata daga mazauna BUK Road, Hauren Wanki, Koki, State Road, Sabon Gari da sauran wurare. Mafi akasarin kararrakin suna da alaka da kwacen waya a adaidaita sahu, satar babur da sauran laifuka, ciki harda yunkurin kisa.”
Ya kara da cewa an kai karar daya daga cikin adaidaitan da aka kama yayin aikin kwace wayoyi kusan sau 10 a cikin maki daya, kuma mammalakinta ya amsa laifinsa da dadewa.
Ya ce daga cikin mutane 28 da aka kama wadanda shekarunsu ke tsakanin 18 zuwa 25, biyu ne kawai suka karyata shan kayan maye.
Sani Ahmad mai shekaru 18 na Kabuga Quarters, wanda ya tona cewa yana shan tabar wiwi da sigari, ya ce ya shafe sama da shekaru biyu yana kwacen waya kuma cewa an kama shi ne yayin da yake kokarin dabawa mutane wuka tare da yi masu fashin wayoyinsu.
Yahaya Musa mai shekaru 20 na Dorayi Quarters ya ce:
“Wannan shine karo na biyar da nake satar wayoyi da adaidaita sahu, kuma zuwa yanzu na kwace wayoyi sama da guda 10 daga mutane. Wannan ne zai zamo na karshe, In shaa Allah.”
Rabiu Sale mai shekaru 18 na Kofar Wambai, ya ce shi dan Magarya ne a jumhuriyar Nijar kuma cewa an kama shi ne bayan ya saci babur a Goron Dutse.
Ya ce:
“Na dade Ina aikata hakan, amma na yi danasanin abun da na aikata a yanzu. Ina so na daina sata.”
Rahoton ya kuma ce bayan sun bayyana laifukansu, Kakakin yan sandan ya ce tuni aka fara bincike kuma za a mika su kotu.
Yan sanda sun ceto tsohon kansilan da yan bindiga suka sace a Nasarawa
A wani labari na daban, mun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Nasarawa ta ce ta ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi, Mista Anthony Duke Effiom, a ranar Lahadi, 30 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan
An yankewa Hedmasta hukuncin share filin kwallo tsawon wata 3 kan satar kudin makaranta
Mista Effiom ya kasance tsohon kansila a karamar hukumar Calabar South da ke jihar Cross River.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Ramhan Nansel, ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya saki a Lafia, babbar birnin jihar Nasarawa, Daily Trust ta rahoto.
Asali: Legit.ng
