Wata sabuwa: Likitocin Najeriya sun sake bijiro da bukata, sun gargadi gwamnati
- Kungiyar Likitoci ta Najeriya ta kara tado da wata magana kan kudaden da mambobinta ke bin gwamnati bashi
- Kungiyar ta ba da wa'adin lokacin da ya kamata gwamnatin ta gaggauta biyan kudaden a cikin wannan shekara
- Wannan na zuwa ne wasu watanni bayan dawowar kungiyar ta likitoci daga wani yajin aiki da suka yi a 2021
Abuja - Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NARD) ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki kan biyan kudaden da aka cire na asusun horas da lafiyar ma’aikatan lafiya na shekarar 2020 (MRTF) ga mambobinta kafin cikar wa'adin kasafin shekarar 2021 a watan Maris 2022.
Kungiyar ta yi wannan kiran ne a ranar Lahadi a cikin wata sanarwar da ta fitar bayan taronta na majalisar zartarwa ta kasa a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.
Sanarwar ta samu sa hannun shugaban kungiyar, Dr Dare Godiya Ishaya; Sakatare Janar, Dr Suleiman Abiodun Isma’il da Sakataren Yada Labarai, Dr Yusuf Alfa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kungiyar ta ce yayin da gwamnati ta biya mambobinta albashin watan Agusta da Satumba na 2021, da kuma MRTF na 2021, har yanzu wasu mambobin ba su sami biyan MRTF na 2020 ba.
A cewar kungiyar:
“Har ila yau, muna burin a kammala biyan MRTF na 2022 kafin jarrabawar kammala karatun digiri na biyu a watan Maris/Afrilu/Mayu 2022 don ba da damar yin amfani da wadannan kudade ta hanyar da mambobinmu ke amfani da su ta hanyar da ta dace."
NARD ta yi kira ga gwamnati, kungiyar gwamnonin Najeriya, masu ruwa da tsaki da kuma ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su nemi gwamnonin jihohin Abia, Imo, Ondo da Ekiti da su gaggauta biyan basussukan da ke kansu.
Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakin dakile wahalar likitoci a kasar, kamar yadda Tribune ta tattaro.
Ta koka da yadda ake fama da karancin ma’aikata a mafi yawan manyan makarantun kiwon lafiya a sakamakon ci gaba da tabarbarewar gata ga likitocin da ke fama da matsalar isassun kudade.
Yajin Aikin NARD: Kungiyar Likitoci Ta Bukaci Shugaba Buhari Ya Sallami Wasu Ministocinsa
A wani labarin, Shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD), Uyilawa Okhuaihesuyi, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sallami duk wanda ke da hannu a yajin aikin da likitoci ke yi a kasar nan.
Okhuaihesuyi yace ya kamata a sallami ministan kwadugo, Chris Ngige, ministan lafiya, Osagie Ehanire, da kuma shugaban MDCN, Tajuddeen Sanusi, matukar ba zasu iya sauke nauyin dake kansu ba.
The Cable ta ruwaito cewa a ranar 2 ga watan Agusta, likitocin suka tsunduma yajin aiki bisa rashin biyansu albashi, da wasu alawus da dai sauransu.
Asali: Legit.ng