Niger: Rayuka birjik sun salwanta, gidaje sun babbake a sabon harin ƴan ta'adda

Niger: Rayuka birjik sun salwanta, gidaje sun babbake a sabon harin ƴan ta'adda

  • Ana zargin mutane da dama sun rasu sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Galkogo da ke karamar hukumar Shiroro a Jihar Neja
  • Yayin tattaunawa da manema labarai, kakakin kungiyar matasan jihar, Jibrin Alawa ya ce sun kai harin tun karfe 3 na yamma har zuwa karfe 6 na ranar Asabar
  • A cewar Alawa, a kalla ‘yan bindiga 200 suka isa kauyen a kan babura dauke da makamai iri-iri suna harbi ko ta ina inda suka babbaka gidaje

Niger - Mutane da dama sun halaka sakamakon farmakin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Galkogo da ke karamar hukumar Shiroro a Jihar Neja.

Yayin tattaunawa da The Cable dangane da mummunan harin, Jibrin Alawa, shugaban kungiyar matasa ta jihar, ya ce harin ya auku ne da misalin karfe 3 na rana har zuwa 6 na yammacin ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Niger: Ƴan ta'addan sun kai sabon hari, sun sheƙe rai 2, sun sace sama da mutum 100

Niger: Rayuka birjik sun salwanta, gidaje sun babbake a sabon harin ƴan ta'adda
Niger: Rayuka birjik sun salwanta, gidaje sun babbake a sabon harin ƴan ta'adda. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Alawa ya ce kusan mahara 200 ne suka afka har kauyen a baburan su rike da miyagun makamai suna harbi ko ta ina.

A cewarsa, maharan sun banka wa gidaje da dama wuta sannan sun kone sansanin ‘Yan Sa Kai da ke kauyen.

“Eh, an kai hari kauyen Kogo yau. Kuma lamarin ya auku ne da misalin karfe 3 na rana. Sun zo da yawan su suna ta harbe-harbe. Mutane sun dinga gudu yayin da wasu suka samu raunuka saboda harbin da ya same su,” a cewar sa.
“Wani ganau ya sanar da ni cewa kafin ya bar kauyen sai da ya kirga gawawwaki bakwai kuma ‘yan bindigan sun babbake sansanin ‘Yan Sa Kai. Sun kai harin ne da misalin karfe 3 na rana kuma sun wuce karfe 6 na yamma. Sun zo da yawansu don sun kai 200 a babura.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa mutane 9 kisar gilla a sabuwar harin da suka kai a Zamfara

“Kun san irin wannan harin kuma kauyen suke hari saboda akwai ‘Yan Sa Kai da dama. Dama an tura su Kontagora daga kauyen don yin aiki na musamman, kwanan su hudu kenan, hakan yasa suka kai wa kauyen farmaki. Kungiyar ‘Yan Sa Kai sun koma kauyen.”

A cewar Ismail Mohammed, kakakin jam’iyyar PDP na karamar hukumar Shiroro, ya ce akwai wasu mazaunan da suka koma garin Kuta Gwada.

“Akwai kauyakun da ake fara samu kafin a zo Galkogo amma mutan Galkogo suka kai wa harin. Yanzu muna kokarin ganin mun je da ababen hawan da za mu ceto mutanen mu da aka sace,” a cewarsa.
“Mutane da dama sun tsere daji. Wasu mutanen sun shige ruwa yayin da wasu suka tsere inda ba a sani ba. Suna da bindigogi kuma sun zo da yawan su a babura suna harbi ta ko ina inda suka lalata gidaje da dama.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Sojoji sun kame 'yan daba cikin mota gabanin zaben gwamnan Ekiti

“Mun san gwamnati ta na kokarin ta amma mutanen mu ba su da kwanciyar hankali. Yanzu haka an kai wasu jama’a Kuta yayin da wasu suka tsere garin Gwada.”

Yayin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan Jihar, ya bukaci The Cable ta tuntubi sojojin Najeriya don jin ta bakin su.

Sai dai ba a samu tattaunawa da Onyema Nwachukwu, kakakin soji ba har lokacin rubuta wannan rahoton.

Niger: Ƴan ta'addan sun kai sabon hari, sun sheƙe rai 2, sun sace sama da mutum 100

A wani labari na daban, ‘yan bindiga sun kai farmaki wasu anguwanni biyu, Fungan Bako da Kawo da ke karkashin karamar hukumar Rafi a Jihar Neja inda suka halaka mutane 2 sannan suka sace mutane fiye da 100.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, cikin wadanda suka sace har da wata mata mai ciki da yarinyar ta mai shekaru biyu.

Kara karanta wannan

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kone gine-gine 110 a Chibok, Zulum ya je ziyarar jaje

Sai dai bayan matar ta sha tafiya a kasa na tsawon lokaci sun sako ta amma sun tsere da diyar ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng