Tun 2014, ba amo balle labarin ƴam matan Chibok 110, Ƙungiyar KADA

Tun 2014, ba amo balle labarin ƴam matan Chibok 110, Ƙungiyar KADA

  • Wata kungiyar Kibaku da ke garin Chibok a jihar Borno ta koka kan rashin jin duriyar 'yam mata 110 cikin 276 na Chibok da Boko Haram suka sace
  • Shugaban kungiyar KADA, Dauda Iliya, ya koka kan yadda gwamnatin ta yi burus da su kuma ta daina fafutukar neman 'yam matan
  • Iliya ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kafa sansanin sojoji tare da aiko kayan aiki Chibok saboda kullum farmaki ake kai musu

Chibok, Borno - Har yanzu babu amo balle labarin yara mata 110 cikin 276 da Boko Haram suka yi garkuwa da su a 2014, kamar yadda kungiyar Kibaku ta Chibok (KADA) ta sanar.

Kungiyar, wadda ta ke tsaka da fafutukar ganin an saki wadanda aka yi garkuwa da su, ta bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin zantawa da manema labarai a Abuja, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a gwagwaryar da take da matsalolin tsaro, Buhari ya ba da tabbaci

Tun 2014, ba amo balle labarin ƴam matan Chibok 110, Ƙungiyar KADA
Tun 2014, ba amo balle labarin ƴam matan Chibok 110, Ƙungiyar KADA. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban KADA, Dauda lliya, ya ce a cikin yara mata 276 da aka yi garkuwa da su, 57 ne suka yi nasarar kubcewa daga hannun wadanda su ka yi garkuwa da su, Premium Times ta ruwaito.

"Ga dukkan alamu Gwamnatin Najeriya ta yi burus gami da nuna halin ko in kula ga halin da Chibok ta tsinci kanta.
"Tun daga karshen 2012 zuwa wannan lokacin, tarin barna da rasa rayuka da dukiyoyi da yankin ya fuskanta ya bar radadi da tabon da ba zai warke ba ga mutane," in ji shi.

Iliya ya ce sama da mutane 72 sun rasa rayukan su, kuma an yi garkuwa da sama da mutane 407 yayin da aka kona tarin gidaje, guraren sana'a da majami'u, inda aka sace ababen hawa sama da 20 bayan tarin ma'ajiyar hatsi da aka lalata.

Kara karanta wannan

Kakakin PDP ya gurfana a gaban kotu kan caccakar gwamnan APC a Facebook

"Daga karshen 2018 zuwa yanzu, yawan hare-hare da barnace-barnace ya wuce misali.
"A wannan shekarar kadai, an kai hari 14 ga watan Janairu a Kautikari( garin da ita ce ta biyu a girma a yankin Chibok) inda aka yi garkuwa da mata biyar, mutane uku, yayin da aka kona tarin gidaje da majami'u.
"Yayin bayyana kalubalen da suka fuskanta, an kai hari a Piyemi, wani babban gari a yankin Chibok, a 20 ga Janairu, inda a kai awon gaba da mutane 19 kusan duka mata da mutum daya, shugaban yan sa ka,,"a cewar sa.
"Mu na sa rai sauran yaran mu mata guda 110 da aka yi garkuwa da su a shekarar 2014 da tarin sauran da aka kwashe lokuta daban-daban za a dawo mana da su.
"Muna rokon gwamnatin tarayya da ta gaggauta kafa sansanin mayaka a garin Chibok kuma ta bude wurin koyar da sana'oin hannu a Chibok saboda gudun yunwa da fatara.

Kara karanta wannan

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kone gine-gine 110 a Chibok, Zulum ya je ziyarar jaje

"Muna bukatar gwamnatin tarayya da ta aiko da rundunar sojoji da kayan yaki ga Chibok dan datse cigaba da kai hare-hare a yankin.
"Muna neman agajin Gwamna gare mu da ya kara kokarin da yake dan ganin an shirya gami da taimakawa mutanen mu dan ganin an tsare mana jiha baki daya musamman Chibok," a cewar iliya.

Yan ta'addan Boko Haram sun kai farmaki Askira Uba, mutane sun gudu daga muhallansu

A wani labari na daban, mazauna garin Askira a karamar hukumar Askira Uba sun gudu daga muhallansu a jihar Borno sakamakon harin da yan ta'addan Boko Haram suka kai ranar Laraba.

Daily Trust ta ruwaito cewa yan ta'addan sun dira garin ne da safiya kuma suka fara kona gidajen mutane.

Yayin da mazauna suka tsere daga muhallansu zuwa cikin daji da tsaunika, jami'an Sojoji sun isa don ceton rayuwar sarkin garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng