Abokin Tanko da suka girma tare: Yadda makashin Hanifa ya ci amana ta shekaru da suka gabata

Abokin Tanko da suka girma tare: Yadda makashin Hanifa ya ci amana ta shekaru da suka gabata

  • Wani abokin abokin Abdulmalik Tanko, makashin Abubakar Hanifa ya bayyana wata cin amana da ya masa shekaru da suka gabata
  • Dahiru Sani, wanda ya ce unguwa daya suka taso tare da Tankon ya ce ya taba karban bashi daga asusun makaranta sannan ya hada baki da wasu don masa sharri a kore shi
  • Sani ya ce Tanko ya karbi kudin ne domin ya bude shagon biziness centre amma daga baya ya ki biya, ya kuma nemi raba shi da aikinsa a matsayin ma'aji a makarantar

Jihar Kano - Dahiru Sani, abokin Abdulmalik Tanko, makashin Abubakar Hanifa ya bayyana wata cin amana da ya masa a lokacin da suke aiki tare a wata makaranta mai zaman kanta a Tudun Wada, Kano.

Kara karanta wannan

An yankewa Hedmasta hukuncin share filin kwallo tsawon wata 3 kan satar kudin makaranta

Tanko, mai makarantar Noble Kids Academy, ya yi fice ne bayan ya halaka Abubakar Hanifa, wata daliba yar shekara 5 a makarantarsa, rahoton Daily Trust.

Abokin Tanko da suka taso tare: Yadda makashin Hanifa ya ci amana ta shekaru da suka gabata
Abokin Tanko da suka girma tare ya bayyana wata cin amana da ya yi masa shekaru da suka gabata
Source: UGC

Tanko ya ci amanata ta, In ji Sani

A hirar da Daily Trust ta yi da shi, Sani ya ce sun girma a unguwa daya da Tanko.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ya ke bada labarin abin da ya faru a lokacin da suke aiki tare, ya ce:

"Shi ne shugaban makaranta ni kuma ni ni ma'ajin kudade a makarantar. Muna aiki ba matsala kafin ya nemi a bashi kudi daga asusun makaranta yana son ya bude shago a kusa da makarantar fasahar lafiya a shekarar 2015/16.
"Na ba shi aron kudi daga asusun makaranta kuma ya yi alkawarin zai biya cikin kankanin lokaci. Wannan bashin da na bashi yasa ya hada baki da wasu malamai domin a kore ni daga makarantar kafin lokacin biyan kudin.
"A karshe, an kama shi saboda almubazaranci da kudin makaranta, hakan yasa aka kore shi, kuma daga nan ne ya tafi ya bude Northwest Preparatory School a Tudun Murtala."

Kara karanta wannan

Mazauna Kano: Dalilin da yasa aka kori makashin Hanifa daga makarantar da ya koyar shekaru 3 da suka shige

Hakazalika, wani tsohon dalibin Tanko shima ya magantu inda ya ce:

"Ya koyar da mu daga aji na farko zuwa na shida a frimare. Yanzu na kammala jami'a. Yana da kirki. Gidan mu na unguwa daya, don haka yawanci muna zuwa makaranta tare mu dawo tare."

A halin yanzu Tanko yana tsare tare da mutanen da ya hada baki da su.

Yadda jami'an DSS 5 suka taimaka min na yi garkuwa da kwastoma na, Wanda ake Zargi

A wani labarin, kun ji cewa wani Akeem Ogunnubi mai shekaru 42 ya bayyana yadda ya yi garkuwa da wani dan kasuwa a Sabo mai suna Bola cikin ranakun karshen mako, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olawale Olokode dama ya bayar da labari yayin tasa keyar mutumin da ake zargi cewa wasu maza dauke da bindigogi sun sace wani dan canji har cikin ofishinsa a ranar 30 ga watan Disamban 2021 da misalin karfe 5:30 da yamma.

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: An kamo matar makashin Hanifa, an kai ta kotu, amma ta musanta komai

Wanda lamarin ya faru da shi kamar yadda Olukode ya shaida ya ce sun zarce da shi daji ne sannan suka bukaci kudin fansa kafin su sake shi, a nan su ka yi masa kwacen N204,000 sannan suka tsere suka bar shi a wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164