An gano gawarwakin mutane 30 da suka fara ruɓe wa a wani asibiti a Rivers

An gano gawarwakin mutane 30 da suka fara ruɓe wa a wani asibiti a Rivers

  • Masu garkuwa da mutane sun zubar da gawawwakin a yasasshen asibitin gwamnati da ke Elele Alimi, wani gari da ke karkashin karamar hukumar Emohua a cikin Jihar Ribas
  • Shugaban karamar hukumar, Dr. Chidi Lyold ya bayyana wannan mummunan labarin a ranar Alhamis tare da wasu jami’an tsaro yayin binciken ‘yan ta’addan da ke yankin
  • Majiyoyi sun bayyana yadda asibitin ya zama maboyar ‘yan ta’addan da ke cin karen su babu babbaka a yankin, kuma ana kyautata zaton gawawwakin wadanda aka yi garkuwa da su ne

Jihar Rivers - An tsinci gawawwakin mutane a wani yasasshen asibitin gwamnati da ke Elele Alimini wacce anguwa ce a karamar hukumar Emohua, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban karamar hukumar, Dr Chidi Lyold ne ya sanar da wannan bakin labarin a ranar Alhamis tare da jami’an tsaro yayin da ya kai ziyara garin don binciko ‘yan ta’addan da suka addabi jama’a.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare hanya sun sace mutane 5 a Jihar Yobe

Majiyoyi sun sanar da yadda asibitin ya koma maboyar ‘yan ta’addan inda suke baje kolin su.

An gano gawarwakin mutane 30 da suka fara rubewa a wani asibiti a Rivers
An gano gawarwakin mutane 30 da aka yi garkuwa dasu a Rivers. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

A cewar Lyold kamar yadda ya sanar a wata takarda ta sakataren watsa labaran sa, Bright Elendu, mamaki ya kama sa bayan ganin rubabbun gawawwakin jama’an da ake zargin garkuwa da su aka yi.

Yayin binciken an gano wasu barayin man fetur

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takardar ta nuna cewa:

“Gawawwaki da dama sun riga sun rube a wani wani gini da ke cikin asibitin, shugaban karamar hukumar ya bukaci jami’an tsaro su bincike gaba daya asibitin wanda ‘yan ta’adda suka mayar maboyar su.
“Shugaban karamar hukumar ya bayyana yadda aka kama wasu barayin man fetur yayin da jami’an tsaron suke ayyukan su.

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Gwarazan Sojoji sun halaka dandazon mayakan ISWAP, sun tarwatsa sansanin su a Neja

“Shugaban tare da jami’an tsaron sun kama wasu direbobi guda biyu wadanda suka yi lodin man fetur na sata a daidai kwanar Rumuekpe kusa da titin East-West.”

Shugaban karamar hukumar ya daura laifin akan shugabannin anguwar wadanda a idanun su ake ta’addanci

Lyold ya daura laifin akan shugabannin anguwannin wadanda suke barin ana tafka barna a anguwannin su sannan ya lashi takobin kama duk wasu masu hannu a laifin.

An yi kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’an ‘yan sandan jihar, DSP Irene Koko, har yanzu hakan bai yuwu ba don bata dauki waya ba kuma bata bayar da amsar sakon da aka tura mata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel