Da duminsa: Uwargidar Sanata Teslim Folarin, ta rigamu gidan gaskiya

Da duminsa: Uwargidar Sanata Teslim Folarin, ta rigamu gidan gaskiya

  • Sanata Teslim Folarin na jihar Oyo ya rasa kyakkaywar matarsa Angela Nwaka a yau Juma'a
  • Folarin wanda ke wakiltar mazabar Oyo ta tsakiya ya sanar da hakan ta bakin mai magana da yawunsa
  • Angela Nwaka ta mutu ne a kasar Birtaniya tana cikin koshin lafiya

Oyo - Angela Nwaka Folarin, Uwargidar dan majalisar dattawa mai wakiltar Oyo ta tsakiya, Teslim Folarin, ta rigamu gidan gaskiya.

Mai magana da yawun Sanatan, YSO Olaniyi, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki na sanar da mutuwarta, TheNation ta ruwaito.

Yace:

"Cikin tawakkali da mika wuya ga Allah mai girma, muna sanar da mutuwar matarmu, uwa garemu kuma yar uwa, Chief (Barr.) Angela Nwaka Folarin."
"Matar Sanata mai wakiltan Oyo ta tsakiyan ta mutu ne ranar Juma'a. Ta mutu a kasar Birtaniya."

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: Ganduje ya sake martani kan kisan Hanifa, ya ce dole ne a yi adalci

"Lafiyarta kalau kafin mala'ikan mutuwa ya kwankwasa kofarta."

Da duminsa: Uwargidar Sanata Teslim Folarin, ta rigamu gidan gaskiya
Da duminsa: Uwargidar Sanata Teslim Folarin, ta rigamu gidan gaskiya
Asali: Facebook

Gwamna ya caccaki tsofaffin da ke kwalamar kujerar Buhari

A wani labarin kuwa, Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo, ya ce ‘yan takarar da ke da “jini a jika” na mulkar Najeriya ne kadai ya kamata a zabe su a zaben 2023 mai zuwa.

Da yake magana a ranar Talata a wurin bikin ritayar da aka yi na karrama Samson Ayokunle, shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Makinde ya ce mulki ba abu ne mai sauki ba.

Ya shawarci masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a shekarunsu na 70 da su yi tunani mai zurfi game da shawarar da suka yanke.

Ya bukaci al’ummar Oyo da ‘yan Najeriya baki daya da su zabi wadanda suke da karfin yi wa kasa hidima da gaske.

Asali: Legit.ng

Online view pixel