Hajji da Umrah: Kasar Saudi Arabia za ta dage takunkumi kan jiragen Najeriya, Jakada

Hajji da Umrah: Kasar Saudi Arabia za ta dage takunkumi kan jiragen Najeriya, Jakada

  • Kasar Saudi Arabia ta ce ta kusa dage dokar dakatar da jirage dauke da ‘yan Najeriya daga shiga kasar don mahajjata su samu damar yin hajji a kasar mai tsarki
  • Jakadan Saudiyya da ke Najeriya, Mr Faisal Bin Ibraheem Al-Ghamidy ne ya sanar da hakan yayin wata ziyara da hukumar Hajji ta Kasar Najeriya, NAHCON ta kai ofishin sa a Abuja
  • Kamar yadda Saudiyya ta nuna, ta sanar da dokar dakatar da jirage daga Najeriya zuwa Saudi Arabia ne don hana yaduwar wata nau’in cutar COVID-19 ne

Saudi Arabia ta ce za ta dage dokar da ta kafa ta dakatar da jiragen sama daga Najeriya zuwa kasar don bai wa masu niyyar zuwa Hajji damar yin bautar.

Jakaden Saudiyya a Najeriya, Mr Faisal Bin Ibraheem Al-Ghamidy ne ya sanar da hukumar hajji ta kasar Najeriya, NAHCON a lokacin da ta kai masa ziyara ofishin sa da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta soke sababbin gyare-gyaren da Majalisa tayi a kasafin kudin 2022

Hajji da Umrah: Kasar Saudi Arabia za ta dage takunkumi kan jiragen Najeriya, Jakada
Hajji da Umrah: Kasar Saudi Arabia za ta dage takunkumi kan jiragen Najeriya, Jakada. Hoto daga saudigazette.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A watan Disamban 2021 ne Saudiyya ta sanar da dokar dakatar da jiragen sama daga Najeriya zuwa Saudiyya a kan yaduwar sabuwar nau’in cutar COVID-19.

Ya ce: “Ina sa ran dakatar da jirage daga Najeriya zuwa masarautar ya kusa karewa.”

Ya yi magana dangane da biyan diyya ga ‘yan uwan wadanda suka samu hatsarin jirgin sama a watan Satumban 2015 a Makkah, wanda ya yi sanadin mutuwar mahajjata fiye da dari.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya ce kasar sa za ta jajirce wurin biyan ‘yan uwan wadanda suka mutu da zarar an tattara bayanan mamatan.

Dama Shugaban NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya yaba a kan alaka da fahimtar junan da ke tsakanin kasashen guda biyu.

Ya bukaci masarautar ta dage dokar dakatar da ‘yan Najeriya don samun damar yin hajji da umra ga maniyyata.

Kara karanta wannan

Masu jini muke so: Gwamna ya caccaki tsofaffin da ke kwalamar kujerar Buhari

Ya kuma mika godiyar sa ga Saudi Arabia a kan kokarin ganin ta biya ‘yan uwan wadanda suka rasu diyyoyin su.

UAE ta sanar da ranar ɗage takunkumin shiga ƙasar ga ƴan Najeriya

A wani labari na daban, hadaddiyar Daular Larabawa, UAE, ta ce za ta cigaba da barin fasinjoji daga kasashen Afrika 12 da suka hada da Najeriya shiga kasar daga ranar Asabar, 29 ga watan Janairu.

Hukumar taimakon gaggawa ta kasar UAE, NCEMA, ta sanar da hakan ne a wata wallafa da ta yi a shafin ta na Twitter a ranar Laraba.

"Daga ranar 29 ga watan Janairu, UAE za ta karba fasinjoji daga kasashen Kenya, Tanzania, Ethiopia, jamhuriyar Congo, Afrika ta kudu, Botswana, Eswatini, Lesotho, Mozambique, Namibia da Zimbabwe," wallafar ta ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng