Rikicin hijabi: Tilas ake son mana, ba mu amince da saka hijabi a makarantun kiristoci ba, CAN

Rikicin hijabi: Tilas ake son mana, ba mu amince da saka hijabi a makarantun kiristoci ba, CAN

  • Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, reshen Jihar Kwara ta musanta amincewa da amfani da Hijabi a makarantun Kiristoci ga dalibai mata inda tace gwamnatin jihar ce ta nemi tilastawa
  • Kungiyar CAN din a wata takarda wacce mukaddashin shugabanta, Bishop Sunday Adewole da Sakataren kungiyar, Rabaran Dr Reuben Ibitoye suka bai wa manema labarai a Ilorin suka bayyana hakan
  • Sakataren da shugaban kungiyar sun ja kunnen gwamnatin Jihar akan bi a hankali dangane da tilasta sa hijabi ga makarantun kiristoci don gudun tayar da tarzoma a Jihar kamar wacce aka taba yi a baya

Kwara - Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, reshen Jihar Kwara ta musanta amincewa da amfani da hijabi ga dalibai mata a makarantun kiristocin da ke jihar inda tace gwamnatin ce ta tilasta dokar, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kakakin PDP ya gurfana a gaban kotu kan caccakar gwamnan APC a Facebook

Kungiyar Kiristocin a wata takarda wacce mukaddashin shugaban kungiyar da Sakataren, Bishop Sunday Adewole da Rabaran Dr Reuben Ibitoye suka bai wa manema labarai a Ilorin a ranar Alhamis sun bukaci gwamnatin jihar akan bin dokar a hankali don gudun tayar da tarzoma.

Rikicin hijabi: Tilas aka mana, ba mu amince da saka hijabi a makarantun kiristoci ba, CAN
CAN ta ce baa amince da sanya hijabi a makaratun kiristoci ba, tilas aka yi mata a Kwara. Hoto: Vanguard NG
Asali: UGC

Kungiyar ta kiristoci da sauran makarantun da ke jihar ta kula da yadda takardar ta shaida cewa ba za su bar wata daliba mace ta sanya hijabi a makarantun su ba.

Kada hakan ya janyo rikici kamar wanda ya taba aukuwa a baya

Takardar ta kara da jan kunnen gwamnati akan kada ta zake wurin tilasta dokar don gudun kawo rikicin addini kamar yadda ta yi a baya.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito takardar tazo:

“Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, reshen Jihar Kwara dangane da batun sanya Hijabi ga dalibai mata na makarantar kiristoci ta Oyun Baptist High School, Ijagbo ta bayyana damuwar ta.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Gwamnatin Kwara ta amince mata musulmai suke sanya hijabi a makarantu

“Idan ba a manta ba, irin wannan rikicin ya auku a watan Maris/Afirilun 2021 cikin Ilorin kuma har ya janyo aka dinga lalata cocina sannan kiristoci da dama suka rasa rayukansu.
“Masu ruwa da tsaki sun dinga kiran taro kashi-kashi don kawo zaman lafiya da fahimtar juna.
“Rikicin nan na OBHS da sauran makarantun kiristoci a Oyun da karamar hukumar Offa yana kara zafi hakan yasa ake neman gwamnatin Jihar ta sanya baki don kada a fara karya dokoki.
“Muna kara tabbatarwa, babu wata makarantar kiristoci da ke Kwara da ta amince da dalibanta su yi amfani da Hijabi wanda gwamnatin Jihar ta tilasta.”

Babu wani taro da gwamnati ta yi da hukumomin makarantun kiristocin

Takardar ta ci gaba da karyata batun wani taro da ma’aikatar ilimin jihar kamar yadda gwamnatin tace ta yi taron da kungiyar kiristoci a ranar 24 ga watan Janairun 2022 a ofishin ta, hakan ba gaskiya bane a cewar CAN.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Rikici ya barke a Legas, gwamnati ta dakatar kungiyar sufuri ta NURTW

A takaice dai kungiyar CAN tare da kungiyar masu makarantun kiristoci na Jihar Kwara sun ce ba su amince da amfani da hijabi a ko wacce makaranta ba.

Kungiyar Kirista Ta Najeriya Ta Buƙaci Buhari Ya Janye Tallafin Man Fetur Kafin 2023

A wani labarin, kun ji cewa Kungiyar Kirista ta Najeriya, NCF, gammayar mabiya Katolika da Protestant ta ce ya zama dole gwamnatin tarayyar Najeriya ta jajirce ta ceto kasar daga rushewa ta hanyar cire tallafin man fetur, .

NCF ta ce akwai alamu kwarara da ke nuna cewa idan an cire tallafin man fetur, da aka ce yana lashe kimanin Naira biliyan 250 duk wata, tattalin arzikin zai shiga mummunan hali, Guardian ta ruwaito.

A wani taron manema labarai a Abuja, shugaban NCF, Bishop John Matthew, tare da sauran shugabannin kungiyar, sun ce tallafin man fetur babban kallubale ne da ya kamata a tunkare shi gadan-gadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164