Iyayen mutumin da ya kashe Hanifa sun gudu daga gidansu saboda tsoron hari

Iyayen mutumin da ya kashe Hanifa sun gudu daga gidansu saboda tsoron hari

  • Iyayen Abdulmalik Tanko, makashin Hanifa Abubakar sun tsere daga gidansu da ke Tudun Murtala a jihar Kano
  • An tattaro cewa sun bar gidan nasu ne saboda yunkurin da aka yi na kai masu farmaki
  • Mazauna unguwar sun ce ba su san takamaiman wurin da iyayen nasa suka koma ba a yanzu

Kano - Wani rahoton Daily Trust ya nuna cewa iyayen mutumin da ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai shekaru 5, Abdulmalik Tanko, sun gudu sun bar gidansu kan tsoron kai masu farmaki.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a lokacin da ta ziyarci yankunan Tudunwada da Tudun Murtala inda daga nan ne Abdulmalik ya fito kuma a nan ne gidansu yake, makwabta sun gaza bayar da bayani kan inda iyayensa suka shiga.

Kara karanta wannan

Uwargida ta dannawa mijinta dutsen guga har lahira don ya dirkawa wata ciki

Iyayen mutumin da ya kashe Hanifa sun gudu daga gidansu saboda tsoron hari
Iyayen mutumin da ya kashe Hanifa sun gudu daga gidansu saboda tsoron hari Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Majiyoyi na kusa da iyalan sun bayyana cewa an yi yunkurin kaiwa iyayen Abdulmalik hari sakamakon sacewa da kashe Hanifa da ya yi. Wannan lamari ya sa iyayensa suka gudu suka bar gidansu.

Musa Shehu ya ce:

“Babu wanda zai fada maku ga takamaiman wurin da suke. Sun koma wani wuri da ba a sani ba. Mahaifiyarsa ta ki karban yaransa kuma ta sallama wa duniya shi.”

Ba zan ɓata lokaci na wajen rattaba hannu kan hukunci kashe wanda ya halaka Hanifa, Ganduje

A gefe guda, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, yace ba zai bata lokaci ba wajen zartar da hukuncin kashe Abdulmalik Tanko, idan aka kawo shi kan teburinsa.

A ranar Litinin, Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya yi alƙawarin bin dokar da kwansutushin ya tanadar wajen zartar da hukuncin kisa kan Tanko, bayan kotu ta tabbatar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kisan Hanifa: Ba zan ɓata lokaci ba wajen zartar da hukuncin kisa kan Tanko, Ganduje

Ganduje ya yi wannan furucin ne yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya tare da mataimakinsa, Nasuru Yusuf Gawuna, shugaban masu rinjayi na majalisa, Labaran Abdul da ƙusoshin gwamnati zuwa gidan iyayen Hanifa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng