'Yan bindiga sun yi wa mutane 9 kisar gilla a sabuwar harin da suka kai a Zamfara
- Yan bindiga sun kashe mutane a kalla tara a hare-haren da suka kai a wasu kauyukan Zamfara a daren ranar Lahadi
- Wasu mazauna kauyukan sun tabbatar da hare-haren inda suka ce mata da maza suna ta baro kauyukansu suna zuwa Tsafe don neman dauki
- Har wa yau, yan banga da jami'an tsaro sun yi nasarar dakile harin da 'yan bindigan suka yi nufin kai wa Yandoton Daji
Zamfara - A kalla mutane tara ne aka kashe yayin da wasu da dama aka raba su da muhallinsu a lokacin da yan bindiga suka kai hari a wasu garuruwa a karamar hukumar Tsafe na Jihar Zamfara.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa wani hatsabibin shugaban yan bindiga mai suna Adamu Aleru ne da ke dajin Tsafe ya ke addabar garuruwa da ke karkashin Tsafe a Zamfara da Faskari a Katsina.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani mazaunin Tsafe, Salisu Sabo, ya shaida wa Premium Times cewa kauyukan da aka kai wa hari a daren Lahadin sun hada da Magazawa, Kajera, Unguwar Dan Halima, Unguwar Rogo, Unguwar Ango, Kurar Mota da Kauyen Kane duk a yankin Bilbis.
Ya ce:
"Sun kai hare-haren ne a lokaci guda, amma inda suka fi kai hari mai muni shine kauyen Magazawa inda aka kashe mutum bakwai. An gano gawarwakin su da safiyar ranar Litinin. A wasu kauyukan ba mu ji an yi kisa ba, amma mafi yawancin yan garin sun gudo zuwa Tsafe. Na ga fiye da mata 50 suna shigowa Tsafe a safiyar yau."
Wani majiyar, daga Tsafe, Mustapha Sani, ya ce harin ya ritsa da yan uwansa da suka tafi daurin aure a Magazawa.
Kalamansa:
"Yan uwan mu maza da mata suna cikin mawuyacin hali a hannun yan bindiga. An fada min an gano gawarwaki bakwai kusa da Magazawa yayin da an gano wasu biyu a Unguwar Kane."
Yunkurin kai hari Yandoton Daji
Mr Sabo ya kuma ce yan bindigan sun yi yunkurin kai hari Yandoton Daji a daren ranar Lahadi amma yan banga da jami'an tsaro suka dakile harin.
Ya kara da cewa yan bindigan sun isa Yandaton Daji misalin karfe 2 na dare amma yan bangan suka fatattake su.
"A yayin da suka gaza shiga garin, sun koma sansaninsu da ke Dajin Munhaye."
Kakakin yan sandan Jihar Zamfara, Mohammed Shehu, bai amsa kirar da sakon kar ta kwana da aka masa ba don jin ba'asi game da harin.
An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona
A wani labarin, wasu mahara sun kashe wani mahaifi da 'ya'yansa su biyu, a ranar Alhamis a hanyarsu ta koma wa gida daga gona a garin Ore a kan hanyar Ore Egbeba a karamar hukumar Ado, jihar Benue.
Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu garuruwa da ke kewayen Ado da ke da iyaka da jihar Ebonyi inda ake rikicin kan iyaka sannan ake fama da matsalan hari daga makiyaya.
Mazauna garin sun ce wannan mummunan kisar da aka yi wa yan gida daya; Mr Enogu, Chigbo Enogu da Sundaya Enogu, ya jefa mutanen cikin tsoro ta yadda ba su iya fita su yi harkokinsu yadda suka saba.
Asali: Legit.ng