'Yan sanda: Jerin sunayen mutum 21 da ake nema ruwa a jallo kan sace basaraken Anambra

'Yan sanda: Jerin sunayen mutum 21 da ake nema ruwa a jallo kan sace basaraken Anambra

  • Rundunar yan sandan jihar Anambra tana neman wasu mutane 21 ruwa a jallo
  • Ana neman mutanen ne a kan kisan wasu mutane biyu da kuma sace basarake a garin Ogwuaniicha da ke karamar hukumar Ogbaru na jihar
  • Kakakin yan sandan jihar, Toochukwu Ikenga, ne ya sanar da hakan inda ya bukaci duk wanda ke da bayanin da zai taimaka ya je ofishin yan sandan jihar

Anambra - Rundunar yan sandan jihar Anambra ta kaddamar da sunayen mutane 21 da ake nema ruwa a jallo kan kisan wasu mutane biyu a garin Ogwuaniicha da ke karamar hukumar Ogbaru na jihar.

Ana kuma zargin mutanen da alaka da sace basaraken garin, Igwe Oliver Chike Nnaji, Sahara Reporters ta rahoto.

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Gwarazan Sojoji sun halaka dandazon mayakan ISWAP, sun tarwatsa sansanin su a Neja

'Yan sanda: Jerin sunayen mutum 21 da ake nema ruwa a jallo kan sace basaraken Anambra
'Yan sanda: Jerin sunayen mutum 21 da ake nema ruwa a jallo kan sace basaraken Anambra Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yayin da yake ambatan sunayen mutanen, kakakin yan sandan jihar, Toochukwu Ikenga, ya bukaci duk wanda ke da bayanai masu amfani kan inda wani daga cikin mutanen yake ya kai rahoto ofishin yan sanda, rahoton Daily Post.

Jawabin ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Rundunar yan sandan jihar Anambra na fatan ayyana neman wadannan mutane ruwa a jallo a binciken da ke gudana na zargin kisan Cif Ajieh Anthony Nwanasor, Ikenna Ugochukwu da kuma sace basarake, Igwe Oliver Chike Nnaji (Ezechukwukwadolu the III) na garin Ogwu-aniocha, karamar hukumar Ogbaru.
"Kwamishinan yan sanda, Echeng Echeng, ya ba yan Anambra da yan garin Ogwu-aniocha tabbacin cewa rundunar ba za ta kyale komai ba a binciken da ke gudana.
"Ya kuma ba al'umma kwarin gwiwar kiran rundunar yan sandan jihar Anambra idan aka samu wani bayani da zai taimaka wa binciken. Za a boye mutum."

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kama mutane 28, sun kwato makamai da layoyi a jihar Neja

Wadanda ake neman sun hada da: Okwudili Ogana, Chidi Ekpendu, Chukwunonso Udom, Amaechi Akachukwu, Emmanuel Ejiofor, Christian Udeze, Chikezie Onwuka aka Osy Torture, Iweka Odogwu, Chimezie Okonkwo aka Danger da Onochie Nwabugwu aka Young PG.

Sauran sune; Anayo Ubadi aka Agunechimba, Chibueze Egwenu, Charles Obi, Aboy Udom, Chinedu Collins Nwonani, Onyebuchi Umuna aka Omeke, Ifeanyi Mbanugo aka Acid, Sunday Osadebe, Nduba Chibuzor, Amechi Adama da Azuakonam Anyakodia.

Yadda wani ya sa aka yi garkuwa da ‘yar uwarsa ta jini wajen neman abin Duniya a Kaduna

A wani labarin, mun ji cewa Hajiya Binta Mohammed ta na shaidawa babban kotun jihar Kaduna da ke Dogarawa cewa Abubakar Haliru ya kitsa dauke ta da aka yi.

Ana zargin Abubakar Haliru wanda kakansu daya da wannan ‘yar kasuwa da shirya yadda za a sace ta. Wannan laifi ya saba sashe na 246 na dokar final kwad.

Lauyar da ta shigar da kara a kotun na Dogarawa da ke Zaria, Jummai Dan-Azumi ta ce ta na da shaidu hudu da za su bada shaida, ta fara da Binta Mohammed.

Kara karanta wannan

Dubun wani matashin saurayi da ake zargi da kashe budurwarsa ya cika

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng