Tun da an ki yarda a kara farashin mai, zamu cigaba da cin bashi kenan: Fadar Shugaban kasa

Tun da an ki yarda a kara farashin mai, zamu cigaba da cin bashi kenan: Fadar Shugaban kasa

  • Fadar shugaban kasa ta bayyana abinda za tayi tun da yan Najeriya sun ki yarda a kara farashin mai
  • Bashin da Najeriya ta ciyo daga hannun bankuna, kasashe, da mutane ya kusa Naira tiriliyan 40
  • Don gudun haka, gwamnatin tarayya na shawarar kara farashin man fetur don daina biyan kudin tallafi

Abuja - Najeriya zata ciyo basussukan kudi sakamakon dakatad da shirin kara farashin man fetur ta hanyar cire tallafin mai, fadar shugaban kasa ta bayyana ranar Laraba.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a hirar da yayi a tashar ChannelsTV.

A cewarsa, ko yan Najeriya sun so ko sun ki, dole a nemo kudi ta wani hanya.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Malaman makarantun firamare a Abuja sun tsunduma yajin aiki

Yace:

"Ko ta kaka, yan Najeriya zasu ji a jika. Ko dai mu fahimta mu bari a cire tallafin mai, ko kuma a cigaba da ciyo basussuka, kuma gwamnatin tarayya da na jihohi zasu fuskanci rashin kudi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba karamin kudi za'a samu ba idan aka cire tallafin mai kuma za'a yi amfani da su wajen ayyukan jin dadin rayuwa. Amma idan muka ki hakan yanzu - kuma na yarda hakan da kamar wuya, to zamu ji a jika."
"Amma ba don siyasa aka dakatar ba."

Fadar Shugaban kasa
Tun da an ki yarda a kara farashin mai, zamu cigaba da cin bashi kenan: Fadar Shugaban kasa Hoto: Mr Adesina

A ranar Litinin, Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur har sai baba ta gani.

Zainab Ahmed, ministar kudi, kasafi da tsarin kasa, ta sanar da hakan a wani taro da aka yi a majalisar dattawan kasar nan a Abuja a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

2023: Miyetti Allah ta ce ta na bayan Tinubu, ta bayyana taimakon da ya yi mata a baya

Shugaban majalisar dattawan, Ahmed Lawan tare da karamin ministan man fetur, Timipre Sylva gami da manajan daraktan NNPC, Mele Kyari, duk sun halarci taron.

Kawo karshen Satumba 2021, ana bin Najeriya jimillar bashin N38.005tn

Ofishin Manejin basussukan Najeriya DMO ta bayyana cewa kawo karshen Satumban shekarar nan ta 2021, ana bin Najeriya bashin N38.005tn.

Wannan na kunshe cikin jawabin da DMO ta saki a shafinta na yanar gizo ranar Talata.

Jawabin yace:

"Bisa al'ada, Ofishin Manejin basussukan Najeriya DMO ta wallafa jimillar basussukan da ake bin Najriya kawo 30 ga Satumba, 2021."
"Wannan ya hada da basussukan gida da na waje, jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya."
"Bashin ya zauna a N38.005tn ko $92.626bn kawo karshen rubu'i na 3 na shekarar 2021."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng