Kawo karshen Satumba 2021, ana bin Najeriya jimillar bashin N38.005tn

Kawo karshen Satumba 2021, ana bin Najeriya jimillar bashin N38.005tn

  • Bashin da Najeriya ta ciyo daga hannun bankuna, kasashe, da mutane ya kusa Naira tiriliyan 40
  • Duk da gwamnati na shirin karban wasu basussukan a sabuwar shekaran nan ta 2022
  • Don gudun haka, gwamnatin tarayya na shawarar kara farashin man fetur don daina biyan kudin tallafi

Abuja - Ofishin Manejin basussukan Najeriya DMO ta bayyana cewa kawo karshen Satumban shekarar nan ta 2021, ana bin Najeriya bashin N38.005tn.

Wannan na kunshe cikin jawabin da DMO ta saki a shafinta na yanar gizo ranar Talata.

Jawabin yace:

"Bisa al'ada, Ofishin Manejin basussukan Najeriya DMO ta wallafa jimillar basussukan da ake bin Najriya kawo 30 ga Satumba, 2021."
"Wannan ya hada da basussukan gida da na waje, jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya."

Kara karanta wannan

Ado Doguwa ya samu karuwar 'diya na 28, ya lashi takobin haifan 30 kafin 2023

"Bashin ya zauna a N38.005tn ko $92.626bn kawo karshen rubu'i na 3 na shekarar 2021."

Tsakanin Yuni da Satumba, bashin ya tashi da N2.540tn.

Buhari da DMO
Kawo karshen Satumba 2021, ana bin Najeriya jimillar bashin N38.005tn
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel