Labari mai dadi: Sojoji sun gano wata kasuwa da mafakar ISWAP, sun kone su kurmus

Labari mai dadi: Sojoji sun gano wata kasuwa da mafakar ISWAP, sun kone su kurmus

  • Sojojin Najeriya sun samu nasarar dura mafakar 'yan ta'addan ISWAP, sun fatattaki 'yan ta'adda da dama
  • Rundunar sojin ta shaida cewa, ta yi kaca-kaca da mafakar, inda ta lalata kayan aikin 'yan ta'addan
  • Ya zuwa yanzu dai rundunar bata bayyana adadin 'yan ta'addan da ta kashe ba ko ta kama, amma ta ce ta lalata abubuwa da dama

Borno - Sojojin Najeriya sun yi nasarar fatattakar 'yan ta'addan ISWAP a wani yankin jihar Borno, inda suka lalata mafakar 'yan ta'addan.

A wata sanarwar da rundunar ta soji ta yada a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa, aikin ya yiwu ne karkashin aikin share fage da sojoji ke yi a yankin.

Sojoji sun grugunta 'yan ta'addan ISWAP
Yanz-Yanzu: Sojoji sun yi kaca-kaca da tushen ISWAP, sun ragargaji 'yan ta'adda | Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

A cewar sanarwar, dakarun rundunar 401 Special Forces Brigade da 19 Brigade Baga ne suka gudanar da aikin a ranar Talara 25 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Sojoji sun kame 'yan daba cikin mota gabanin zaben gwamnan Ekiti

A cewar wani yankin sanarwar:

"Dakarun Sojojin na 401 Special Forces Brigade tare da na 19 Brigade da ke Baga yayin da suke aikin share fage a tsakanin Cross Kauwa da Gudumbali a jihar Borno a jiya 25 ga Janairu, 2022 sun yi nasarar fatattakar 'yan ta'adda tare da lalata mafakar ISWAP."

Hakazalika, rundunar ta ce ta lalata wata shahararriyar kasuwar 'yan ta'addan Boko Haram a yankin Gumsari na Damboa a jihar Borno.

A cewar sanarwar:

"Bugu da kari, da sanyin safiyar yau 26 ga watan Junairu 2022, sojojin 25 Task Force Brigade Damboa, jihar Borno, sun lalata tare da kona kasuwar dare ta BokoHaram/ISWAP a Gumsuri."

Katsinawa sun fada tashin hankali bayan an janye sojoji daga yankunan jihar

A wani labarin, mazauna garin Runka da wasu yankuna na karamar hukumar Safana ta jihar Katsina sun bayyana tsoron su kan makomar su bayan kwashe sojojin yankin da aka yi a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan sanda da mafarauta sun hallaka 'yan bindiga, sun ceto wasu mutane a Adamawa

Sojoji da ke aikin hadin guiwa na tsaro suna da sansani a Runka, gari na biyu mafi girma a karamar hukumar Safana ta jihar, har zuwa jiya Litinin da aka janye su, Premium Times ta ruwaito.

Mazauna yankin sun ce 'yan ta'adda sun sanya wa Runka ido ganin irin tsaro da suke fuskanta, hakan ne kuwa ya kange su daga farmakin miyagun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.