Hukumar Hisbah ta yi nasarar ƙwace kwallaben giya 1,906 a Jigawa
- Jami'an hukumar Hisbah a Jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin kasar sun ce sun kwace kwallaben giya 1,906 a cikin shekarar 2021
- Ibrahim Dahiru, Babban kwamandan hukumar ne ya furta hakan a ranar Talata a Dutse yayin zantawa da manema labarai
- Har wa yau, hukumar kuma ta ce ta kama mutane 92 da ake zargi da aikata ayyukan badala daban-daban da suka hada da caca-caka, karuwanci da sauransu
Jihar Jigawa - Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa, ta ce ta kwace kwallaben giya guda 1,906 daban-daban a samame daban-daban da ta kai a jihar a shekarar 2021, The Punch ta ruwaito.
Kwamandan Hisbah na Jihar, Ibrahim Dahiru, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, a ranar Talata a Dutse.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dahiru ya ce hukumar ta kwace kwallaben giyan ne a wuraren shan giya daban-daban da otel a jihar yayin samame.
Ya ce an kama wadanda ake zargin karuwai ne har su 92 saboda aikata ayyuka na rashin tarbiyya yayin samamen.
A cewarsa:
"An kama wadanda ake zargin saboda ayyukan badala da suka hada da caca, karuwanci da shirya taron rawa ko casu yayin bikin daurin aure da wasu bukukuwan.
"Hukumar ta kuma samu nasarar rufe gidajen badala da dama a jihar a cikin shekarar ta 2021 da ta gabata."
Dahiru, wanda ya jadada cewa an haramtawa mabiya addinin musulunci shan giya a jihar, ya kuma yi kira ga mazauna jihar su kauce aikata munanan ayyuka da sauran abubuwa na badala da ka iya janyo tabarbarewar tarbiyya.
Kano: Motar Giya Ta Faɗi Kusa Da Ofishin Hisbah, Wasu Sun Ƙi Kai Dauƙi Don Gudun Fushin Allah
A wani rahoton, wata mota kirar Hilux da ke dauke da barasa ta fada cikin kwata da ke daf da ofishin Hisbah a Panshekara, karamar hukumar Kumbotso na jihar Kano.
An rahoto cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Talata 16 ga watan Nuwamba kuma direban motar ya jikkata.
Mazauna yankin sun garzaya domin kai wa mutanen da ke cikin motar dauki ne sannan suka gano ashe giya ne makare cikin motar.
Asali: Legit.ng