Kada dai a samu hanyar tatsar masu makarantun kudi: PDP ta gargadi Ganduje kan batun lasisin makarantun kudi
- Jam'iyyar PDP a Kano ta yi kira ga gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, da kada ya yi amfani da batun soke rijistar makarantu masu zaman kansu wajen tatsar kudade
- PDP ta kalubalanci Ganduje da ya bi ka’idojin da doka ta gindaya na sanya ido tare da gudanar da makarantu masu zaman kansu wajen aiwatar da gyare-gyaren
- Jam'iyyar ta kuma jinjinawa hukumomin tsaro kan yadda suka tafiyar da lamarin kisan Hanifa Abubakar
Kano - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen Kano ta bukaci gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da ta bi ka'ida wajen bita da sabonta lasisin makarantun kudi a jihar.
Jam'iyyar ta ce dama chan akwai tanade-tanade a kasa na tsarin da ake bi bisa doka wajen kafa makarantu masu zaman kansu wanda gwamnatin baya ta Musa Kwankwaso ta samar.
Shugaban jam'iyyar, Shehu Sagagi a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a jihar, ya gargadi gwamnan a kan yin amfani da shirin wajen tatsar kudi daga shugabannin makarantun, Vanguard ta rahoto.
Sagagi ya ce:
"Kan batun sauya fasalin makarantun kudi, PDP na shawartan gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje da ya bi matakan da ya kamata daidai da dokar hukumar kafa makarantun kudi na jihar Kano wacce ke kula da ayyukan makarantun da ba na gwamnati ba a jihar.
“Mun samu labarin cewa Gwamna Ganduje ya janye lasisin dukka makarantu masu zaman kansu a jihar, tare da nuna tawali’u da kishin kasa, don haka za mu so jan kunnen gwamnatin jihar da kada ta yi amfani da wannan damar wajen tatsar kudade daga hannun mamallakan makarantun kudi a jihar.
"Duk da muhimmancin da ke tattare da sake fasalin bangaren ilimi masu zaman kansu wanda ya kamata ace an dade da yi, bai kamata gwamnatin jihar Kano ta dauki matakin a matsayin wata hanyar da za a bi wajen karbar kudade daga hannun masu makarantu ba."
Sagagi ya kuma yaba wa kokarin hukumomin tsaro kan matakin gaggawa da suka dauka a bincike, kamawa da kuma gurfanar da wanda ya kashe Hanifa Abubakar, rahoton BBC Hausa.
Ganduje ya dakatar da lasisin makarantun kudi a Kano
A baya mun kawo cewa, Gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya dakatar da dukkan lasisin makarantun kudi da ke fadin jihar, har sai zuwa lokacin da aka tantance su.
Sanusi Sa'id Kiru, kwamishinan ilimi na jihar Kano ne ya tabbatar da hakan lokacin da ya ke ganawa da manema labarai.
Wannan al'amarin na zuwa ne bayan 'yan sanda sun gurfanar da mamallakin makarantar Noble Kids a gaban kotu, Abdulmalik Tanko, wanda ya amsa kashe Hanifa Abubakar, yarinya mai shekaru biyar, BBC Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng