Rudani: An sauke babban sarki a Bayelsa jim kadan bayan an ceto kwamishina daga hannun 'yan bindiga
- Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya sauke babban sarkin garin Otuokpoti da ke karamar hukumar Ogbia, Cif A.C.T Wongo
- Diri ya kuma maye gurbinsa da Cif Rescue Abe a matsayin mai rikon kwarya
- Matakin gwamnan na zuwa ne bayan an yi nasarar ceto kwamishinan cinikayya da kasuwanci, Mista Federal Otokito, daga hannun yan bindigar da suka yi garkuwa da shi
Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya tube rawanin babban sarkin garin Otuokpoti da ke karamar hukumar Ogbia, Cif A.C.T Wongo inda ya kuma maye gurbinsa da Cif Rescue Abe a matsayin mai rikon kwarya.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kwamishinan cinikayya da kasuwanci, Mista Federal Otokito, ya samu yancinsa a ranar Litinin, 24 ga watan Janairu, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Wadanda suka yi garkuwa da Otokito sun sake shi kwanaki biyar bayan sun yi awon gaba da shi daga gidansa da ke garin Otuokpoti a karamar hukumar Ogbia ta jihar.
Jaridar The Sun ta rahoto cewa wadanda suka yi garkuwa da shi sun sako shi ne bayan sun fahimci cewa asirinsu ya tonu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Babban sakataren labarai na gwamnan, Daniel Alabrah a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce kwamishinan yan sandan jihar Bayelsa, Mista Ben Nebolisa da daraktan hukumar tsaro na farin kaya a jihar, Mista Mohammed Abdullahi, sun gabatar da Mista Otokito ga gwamnan a gidan gwamnati da ke Yenagoa.
Zan sako shi idan 'yan sanda suka saki mahaifina, in ji wanda ya sace Kwamishina
A baya mun kawo cewa, wadanda suka yi garkuwa da kwamishinan cinikayya da kasuwanci na jihar Bayelsa, Mista Otokito Federal Oparmiola, sun tuntubi sarkin garinsa, Otuokpoti a karamar Hukumar Ogbia ta Jihar.
Wadanda suka sace Otokito, wadanda ake ganin suna gudanar da haramtacciyar masana'antar tace mai sun farmaki gidansa da ke garin a daren ranar Alhamis, sannan suka dauke shi daga dakinsa da bindiga zuwa wajen wani kwale-kwale da ke jira a bakin ruwa sannan suka tsere.
An tattaro cewa sun yi garkuwa da Otokito kan ya yi adawa da shirinsu na kafa haramtacciyar masana'antar tace mai a dajin garin.
Asali: Legit.ng