Yanzu-Yanzu: JAMB ta sanar da lokacin da za a fara rajistar UTME da DE na 2022
- A yau Litinin ne hukumar jarrabawa ta JAMB ta fitar da wata sanarwa mai bayyana lokutan da za a yi rajistar UTME da DE na 2022
- Hakazalika, sanarwar ta kuma bayyana lokutan da za a fara jarrabawar gwaji ta Mock da UTME na shekarar
- Sanarwar na zuwa ne yayin da dalibai ke ci gaba da jiran sanarwar lokutan rajista da jarrabawar ta 2022
Abuja - A ranar Litinin ne hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa ta bayyana cewa za a fara rajistar jarrabawar shiga manyan makarantu da jarrabawar shiga kai tsaye na DE a ranar 12 ga watan Fabrairun 2022.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar ta na mako-mako da Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar Dokta Fabian Benjamin ya fitar, Punch ta ruwaito.
A cewar rahoton The Nation, jadawalin abubuwan da za su faru inji sanarwar su ne:
"Za a fara rajistar UME/DE a ranar 12 ga Fabrairu 2022 kuma ta kare 19 ga Maris 2022. Za a yi jarrabawar gwaji ta Mock a ranar 20 ga Afrilu 2022. Jarrabawar UTME kuwa za a yi ta daga 20 zuwa 30 ga Afrilu 2022".
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
JAMB ta kirkiro wasu sabbin darusa a manhajar jarrabawar UTME ta shekarar 2022
A wani labarin, hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta ce za ta gabatar da sabbin darussan kimiyya guda biyu a jarrabawar JAMB, Punch ta ruwaito.
Magatakardar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka ranar Asabar 4 ga watan Disamba a Abuja. Darussan sune Physical Health Education da Computer Science.
Oloyede yace: "Muna tambaya da wayar da kan jama'a, musamman dalibai, wadanda za su yi jarrabawar, cewa wadannan darussa biyu na kimiyya ne da za a kara a zabinsu don fadada damar da masu rubuta jarrabawa zasu iya samun damar shiga manyan makarantu."
Asali: Legit.ng