Zan sako shi idan 'yan sanda suka saki mahaifina, in ji wanda ya sace Kwamishina
- Wadanda suka sace kwamishinan cinikayya da kasuwanci na jihar Bayelsa, Mista Otokito Federal Oparmiola, sun yi kira a waya
- Shugaban maharan wadan ya kira sarkin garin Otuokpoti ya ce zai sako shi amma sai yan sanda sun saki mahaifinsa wanda ke tsare a hannunsu
- Ya kuma yi barazanar dawowa garin idan har ba a cika masa bukatarsa ba
Bayelsa - Wadanda suka yi garkuwa da kwamishinan cinikayya da kasuwanci na jihar Bayelsa, Mista Otokito Federal Oparmiola, sun tuntubi sarkin garinsa, Otuokpoti a karamar Hukumar Ogbia ta Jihar.
Wadanda suka sace Otokito, wadanda ake ganin suna gudanar da haramtacciyar masana'antar tace mai sun farmaki gidansa da ke garin a daren ranar Alhamis, sannan suka dauke shi daga dakinsa da bindiga zuwa wajen wani kwale-kwale da ke jira a bakin ruwa sannan suka tsere.
An tattaro cewa sun yi garkuwa da Otokito kan ya yi adawa da shirinsu na kafa haramtacciyar masana'antar tace mai a dajin garin.
Jaridar Punch ta rahoto cewa shugaban masu garkuwa da mutanen ya kira shugaban garin a wayar tarho sannan ya sanar masa cewa kwamishinan na a hannunsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai basu riga sun kira iyalan wanda abun ya ritsa da shi ba fiye da sa'o'i 48 bayan sun tafi da shi wani wuri da ba a sani ba.
Wata majiya ta iyalan, wacce ta yi magana cike da kwarin gwiwa a ranar Asabar, ta ce shugaban masu garkuwa da mutanen ya kira basaraken da misalin karfe 5:30 na safiyar ranar Asabar.
A cewar majiyar, shugaban kungiyar bai nemi a biya kowani kudin fansa ba amma ya bayyana cewa za su saki kwamishinan bisa sharadin cewa yan sanda su saki mahaifinsa da ke tsare.
Majiyar ta ce:
"Ba su kira iyalan ba amma jagoransu ya kira sarki cewa shine ya yi garkuwa da shi kuma kwamishinan na tare da shi.
"Ya kira sarkin da misalin karfe 5:30 na safe amma bai nemi kudin fansa ba. Abu daya da ya nema shine cewa a saki mahaifinsa da ke tsare a hannun yan sanda. Ya yi barazanar dawowa garin idan ba a cika bukatarsa ba."
Yan bindiga sun je har gida, sun yi awon gaba da Kwamishinan Jiha
A baya mun kawo cewa miyagun yan bindiga sun sace kwamishinan cinikayya da kasuwanci na jihar Bayelsa, Mista Otokito Federal Oparmiola.
Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun yi awon gaba da Mista Otokito, a gidansa dake Otuokpoti, ƙaramar hukumar Ogbia, a daren ranar Alhamis.
Daily Trust ta rahoto cewa yan ta'addan sun farmaki garin ne da misalin ƙarfe 11:00 na daren ranar Alhamis, bayan tsorata mutane, suka shiga gidan kwamishinan.
Asali: Legit.ng