Labari ne mai ban tsoro - Kungiyar tuntuba ta arewa ta yi Allah wadai da kisan Hanifa

Labari ne mai ban tsoro - Kungiyar tuntuba ta arewa ta yi Allah wadai da kisan Hanifa

  • Kungiyar Arewa ta ACF ta yi Allah wadai da mutuwar Hanifa Abubakar, wacce ake zargin shugaban makaranta su da kashe ta a jihar Kano
  • ACF ta bayyana lamarin a matsayin labari mai matukar ban tsoro da bakin ciki
  • Ta yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su dauki mataki kan abubuwan da ke gudana a makarantu a yanzu

Kano - Kungiyar tuntuba ta arewa wato ACF ta yi Allah wadai da mutuwar Hanifa Abubakar, yarinya yar shekara biyar da ake zargin wani shugaban makaranta da kashe ta a jihar Kano, The Cable ta rahoto.

An yi garkuwa da dalibar a watan Disambar 2021 sannan wadanda suka sace ta suka nemi a biya naira miliyan 6 a matsayin kudin fansa.

Yan sanda a Kano sun kama Abdulmalik Tanko, shugaban makarantar su Hanifa wanda ake zargi da kashe ta a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Kisan gillar Hanifa: Gwamna Ganduje ya magantu, ya bayyana matakin da za a dauka

A cewar wata sanarwa a ranar Asabar, 22 ga watan Janairu, daga kakakin kungiyar, Emmanuel Yawe, ACF ta yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su dauki matakan gaggawa domin kawar da illolin da ke addabar al’umma da aikata laifuka a makarantun kasar.

Labari ne mai ban tsoro - Kungiyar tuntuba ta arewa ta yi Allah wadai da kisan Hanifa
Labari ne mai ban tsoro - Kungiyar tuntuba ta arewa ta yi Allah wadai da kisan Hanifa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Yawe ya ce:

"Kungiyar tuntuba ta Arewa tana fatan nuna kaduwarta da rashin jin dadinta kan ayyukan ta'asar da ke gudana a makarantun Najeriya.
"Wadannan sun hada da cin zarafi, kisa, garkuwa da mutane, luwadi, kungiyar asiri da sauransu. Na baya-bayan nan shine zargin garkuwa da kisan daliba yar shekaru biyar, Hanifa Abubakar da malaminta Abdulmalik Muhammed ya yi a wata makarantar kudi da ke Kwanar Dakatar a jihar Kano.
“Wannan labari ne mai ban tsoro kwatankwacin abin da ya faru a watan Disambar shekarar da ta gabata lokacin da dabilai yan uwan Sylvester Oromoni mai shekara 12 a Kwalejin Dowen, suka ci zarafinsa sannan suka azabtar da shi har lahira saboda ya ki shiga cikin ayyukansu na kungiyar asiri.

Kara karanta wannan

2023: Tsohuwar Sanata ta aika saƙo mai tada hankali ga Tinubu, Osinbajo, Atiku da sauran ƴan takara

“Kungiyar tuntuba ta Arewa tana son jawo hankalin hukumomi kan wannan sabuwar annoba ta muggan kwayoyi, ta’addanci, kungiyoyin asiri da kuma mace-mace da ke gudana a fadin makarantun kasar da kuma jefa rayuwar ‘ya’yanmu mata da maza cikin hatsari.
"Wadannan abun tsaro ba su tsaya a iya makarantun kudi ba kawai. Amma mun fi mayar da hankali kan abubuwan da ke wakana a makarantun kudi saboda suna daukar dalibansu tamkar abun da ake siya da kudi ne.
“Wannan mummunar dabi’a ce da ba iya makomar wadannan yaran za ta bata ba harma da Najeriya. Muna kira ga gwamnatocinmu da su shiga lamarin da karfi tare sannan su kawar da wannan yanayi."

Har da hawayen ƙarya: Mai makarantarsu Hanifa ya yaudare mu yayin da ya zo jajen ɓatar ta, Kawun Hanifa

A baya mun ji cewa Abdulmalik Mohammed Tanko, mai makarantar Noble Kids da ke Kwana a Kano ya kai wa iyayen Hanifa Abubakar, dalibar makarantarsa mai shekaru 5, ziyara bayan batan ta a watan Disamba.

Kara karanta wannan

Me yasa ka kashe ta: Mahaifiyar Haneefa da aka yiwa kisan gilla ta farmaki makashin 'yarta

Daily Trust ta ruwaito yadda Tanko da kan sa ya amsa laifukan sa yayin da jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kano suka tasa keyar sa ranar Juma’a.

Ya bayyana yadda ya yi garkuwa da Hanifa ya ajiye ta a cikin gidan sa daga bisani ya sa mata guba a cikin abinci. Bayan nan ya haka rami tare da birne ta a cikin harabar makarantar sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng