Dubun wasu gawurtattun yan leƙen asirin yan bindiga ya cika a Abuja

Dubun wasu gawurtattun yan leƙen asirin yan bindiga ya cika a Abuja

  • Wasu mutum bakwai da ake zargin masu kwarmatawa yan bindiga bayanai ne sun shiga hannu a yankin Abuja
  • Jami'an tsaro sun cafke wani imfoma ɗaya da ya haddasa garkuwa da wani Fulani, hakan ya yi sanadin kama wasu mutum shida
  • Rahoto ya nuna cewa jami'an sun tasa keyar mutanen zuwa ofishin yan sanda dake Lapai a jihar Neja, domin bincike

Abuja - Wasu mutum bakwai da ake zargin masu kwarmata wa yan bindiga bayanai ne sun shiga hannun jami'an tsaro a yankin Abuja.

Daily Trust ta ruwaito cewa haɗakar rundunar jami'an tsaro ta damƙe mutanen ne a Rafindaji, dake karamar hukumar Abaji, a babban birnin tarayya Abuja.

Ƙauyen Rafindaji ya haɗa iyaka da yankin ƙaramar hukumar Lapai dake jihar Neja, kuma rafin Gurara ne kaɗai ya raba yankunan biyu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai mummunan harin rashin imani jihar Neja, sun halaka dandazon mutane

Asirin Imfoma ya tonu
Dubun wasu gawurtattun yan leƙen asirin yan bindiga ya cika a Abuja Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun sace manoma huɗu, kuma suka kashe yan Bijilanti guda biyu cikin kwana biyar a yankin.

Yadda Dubun mutanen ya cika

Wani jami'in tsaro, wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace waɗan da ake zargin imfoman yan bindiga ne sun shiga hannu a ƙauyen Mayaki, da safiyar Alhamis.

Yace kama mutum ɗaya da jami'an tsaro suka yi, shi ne ya yi jagoran kame wasu mutum shida abokan aikin sa.

Yace:

"Cafƙe imfoma ɗaya, wanda yasa aka sace wasu fulani a Rafindaji, shi ne ya yi sanadin kame wasu mutum 6 da suke sana'a ɗaya."

Ya ƙara da cewa tuni aka kai waɗan da aka damƙe ɗin ofishin yan sanda dake Lapai, jihar Neja domin cigaba da bincike.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun bindige Basarake a jihar Arewa har lahira a cikin gidansa

Basarake ya tabbatar da lamarin

Magajin garin Gulida, Sardauna Abubakar, ya tabbatar da nasarar kama mutanen, yace an tafi da su caji ofis ɗin yan sanda na Lapai.

"Eh gaskiya ne, an kama imfoma guda 7 a Rafindaji. Yanzun da nake magana da ku suna can ofishin yan sanda na Lapai a jihar Neja.

Da aka tuntubi kakakin yan sanda na jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ba'a same shi ba, bare mu ji ta bakin hukumar yan sanda ta jihar Neja.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kai mummunan hari hedkwatar APC, sun halaka jiga-jigan jam'iyya, sun sace mutum ɗaya

Yan ta'addan sun yi wa jiga-jigan jam'iyyar ɓarna, inda suka kashe mutum biyu, kuma suka jikkata wasu da dama, suka yi awon gaba da mutum ɗaya.

Wata majiya daga cikin mahalarta taron, ya bayyana cewa an kira taron ne domin sasanci tsakanin bangarorin jam'iyyar APC a kokarin da ake na haɗa kai baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai mummunan hari hedkwatar APC, sun halaka jiga-jigan jam'iyya

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262