Damfarar N299.86m: Kotu na neman wani tsohon dan takarar gwamnan Zamfara

Damfarar N299.86m: Kotu na neman wani tsohon dan takarar gwamnan Zamfara

  • Tsohon dan takarar gwamna a jihar Zamfara ya shiga komar wata kotu a Legas kan zargin sama da fadi da wasu kudade
  • An zargi tsohon dan takarar ne da tafka damfar sama da N299.68m daga wani bankin da ba a bayyana sunansa ba
  • Rahoton da muka samu ya bayyana yadda kotu a baya ta zarge su, har ta kai ga ba da belinsu, amma aka kara tada maganar

Legas - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta gayyaci tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar PPN a jihar Zamfara, Adamu Bashir da wasu mutane biyu domin amsa tambayoyi kan zargin damfarar N299.86m.

Sauran kamfani ne, OBD Petroleum Limited; da Manajan Daraktanta Umeanor Obinna Michael.

Mai shari’a Abimbola Awogboro ya bayar da sammacin ne a ranar Laraba, biyo bayan bukatar da wani babban lauya a ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), Misis Kehinde Bode-Ayeni ya gabatar.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Nnamdi Kanu ya ce shi ba dan IPOB ba ne, bai ma da alaka da ita

Tsohon dan takarar gwamna ya saci kudi
Tsohon dan takarar gwamna a Zamfara ya tafka damfarar miliyoyi, ya shigo komar kotu | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Bode-Ayeni ya yi zargin cewa wadanda ake tuhumar sun gaza zuwa gaban kotu tun bayan tuhumar da ake musu, The Nation ta ruwaito.

Ta kuma roki kotun da ta umarci wadanda ke tsayawa wadanda ake tuhuma da su ba da dalilin kin amsa kiran kotu, kamar yadda sashi na 184 na kundin shari’a na hukumar (ACJA) 2015 ya tanada.

Mai shari’a Awogboro ya amince da bukatar kuma ya dage sauraron karar zuwa ranar 3 ga Maris, domin gurfanar da wadanda ake tuhuma.

A bisa karar da aka yi wa kwaskwarima mai lamba FHC/L/281c/2016, wadanda ake tuhumar a ciki ko a wajen watan Oktoban 2014, sun samu lamuni na N160m da kuma N139.8m daga banki ta hanyar karya da niyyar zamba.

Wadanda ake tuhumar sun yi karyar cewa za a yi amfani da kudin ne wajen samar da lita miliyan 2.2 na AGO ga kamfanin LastaI Energy, Limited.

Kara karanta wannan

Karya ne: NEC ba ta kai ga kara kudin man fetur daga N165 zuwa N300 ba - Osinbajo

A baya dai an gurfanar da su gaban kuliya bisa irin wannan tuhuma a gaban alkalin babbar kotun tarayya mai shari’a Saliu Saidu.

Sun musanta zargin a gaban alkali kuma an ba da belinsu. Bayan da mai shari'a Saidu ya yi ritaya ,an mayar da shari’ar zuwa gaban mai shari’a Awogboro.

Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ya gayyaci EFCC ta binciki kudin gina sakatariya da aka sace

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Okwesileze Nwodo yace kudin da ya damkawa magajinsa domin gina sakatariyar jam’iyya sun bace.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Dr. Okwesileze Nwodo yana cewa Naira biliyan 11.8 da aka ware da nufin ginawa jam’iyyar PDP babban ofishi sun yi dabo.

Okwesileze Nwodo ya yi wannan bayani ne da yake gabatar da takarda a game da yadda ake tafiyar da jam’iyyar a wajen wani taro da aka shirya a Abuja.

Tsohon shugaban na PDP ya yi kira ga hukumomin yaki da rashin gaskiya su yi bincike, a hukunta wadanda suka saci kudi a asusun jam’iyyar adawar.

Kara karanta wannan

Hotunan makusancin ɗan ta'adda Turji, tare da wasu gwamnonin arewa ya tayar da ƙura

A wani labarin, miyagun yan bindiga sun bindige wani tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya, Alhaji Sagiru Hamidu, akan hanyar Kaduna-Abuja.

Aminiya Hausa ta rahoto cewa Alhaji Sagiru Hamidu na daya daga cikin matafiyan da harin yan bindiga ya rutsa da su ranar Lahadi a babbar hanyan.

Rahotanni sun tabbatar da cewa miyagun yan bindigan sun harbi tsohon dan takarar ne yayin da suka bude wuta kan matafiyar da yammacin Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.