'Kazamin sasanci: An kama su da satar man fetur na N200m, za su biya N2000 kacal a sake su, Alƙali ya koka
- Alkalin babban kotun tarayya da ke Warri, Okong Abang ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda masu kara da wadanda aka yi kara suka daure hannun kotu
- Hakan ya faru ne sakamakon wani sasanci da suka yi tsakaninsu aka rage tuhumar da ake yi wa wadanda aka gurfanar da yadda hukuncin laifinsu ya sauya
- Da farko, karar da aka shigar kan wadanda aka kama da satar danyen man fetur na N200m tana dauke da hukuncin daurin rai-da-rai ne
- Daga bisani bangarorin biyu suka sasanta kansu bayan shekaru, masu karar suka sauya tuhumarsu ta yadda tarar N2000 masu laifin za su biya a sake su kuma babu yadda kotu za ta yi
Jihar Delta - An kama barayin man fetur su tara da jiragen ruwansu dauke da danyen man fetur da kudinsa ya kai Naira miliyan 200 a shekarar 2015 amma za a sake su bayan kowannensu ya biya tarar N2000, Premium Times ta ruwaito.
A watan Nuwamban 2021, Babban Kotun Tarayya na Warri, Jihar Delta, ta tsare su a gidan gyaran hali, har zuwa lokacin da suka cika ka'idojin biyan tarar sannan a sake su.
Alkalin da ke shari'ar, Okong Abang, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda wadanda suka shigar da karar da wanda aka yi karar suka hada kai don ganin kotun ta yanke wannan hukuncin a ranar 24 ga watan Nuwamban 2021.
Onyeka Ohakwe, lauya mai shigar da kara daga Ma'aikatar Shari'a ta Tarayya, ta shigar da sabon kara na mai daure kai inda ta ce sun yi sulhu da wanda ake karar, bayan rage tuhume-tuhumen a watan Oktoba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta sauya tuhumar na farko da ke dauke da hukuncin daurin rai-da-rai ta maye gurbinsa da wani da ke dauke da hukuncin biyan tarar N2000 kacal.
"Wane irin gyara ne wannan" alkalin ta ke tambaya yayin yanke hukuncin, yana mai cewa wannan dai ba domin amfanin al'ummar kasa aka yi ba.
Ya bayyana cewa kamata ya yi a sauya hukuncin ya kara tsauri domin karfafa tuhume-tuhumen amma a wannan karon, da na ke gani da farko a rayuwa ta an sauya hukuncin ne domin a saukaka wa wadanda ake tuhumar.
Ainihin shari'ar
Jami'an Sojojin Ruwan Najeriya, ne suka kama barayin danyen man su tara dauke da danyen mai yayin da suke sintiri a Forcados/Escravos, Ogulaha, Jihar Delta a ranar 11 ga watan Nuwamban 2015.
Da farko, mutane 12 aka kama, amma daga baya aka saki uku cikinsu kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Sauran taran da ofishin Antoni Janar na Tarayya ta gurfanar a kotu sune: Adeola Goodness Olanimiji, Olaoluwa Temitope, Kelvin Onyeka, Dare Lukman, Ibrahim Sese, Amaechi Nkwocha, Anayo Chukwu Ejiogu, Emmanuel Ekuma, da Lucky Urhie.
An gurfanar da su tare da jirgin ruwansu mai lamba 7323473.
Bayan Sojojin Ruwan sun yi bincike, sun mika su ga yan sanda daga bisani kuma ofishin Atoni Janar na kasa ta karbi shari'ar.
Masu shigar da karar sun sauya tuhumar. An kama su ne da danyen mai mai nauyin ton 4,000 a Jihar Delta.
Cikin shekaru biyar, masu shigar da karar karkashin jagorancin Ms Ohakwe sun sauya karar domin yin sasanci da wadanda aka yi karar.
An sauya karar na farko da wata wanda aka rage tuhume-tuhumen uku zuwa daya kawai wacce hukuncin kawai ba zai wuce tarar N2000 ba.
Mr Abang ya ce masu karar sun sauya tuhumar na farko mai dauke da daurin rai-da-rai zuwa wacce ke dauke da hukuncin tarar N2000 kawai.
Kazamin sasanci
Baya da asarar kudi da laifin ya janyo a kasa, satar danyen mai yana kawo matsaloli ga muhalli da rayukan mutane da manoma da kifi da sauran dabobin ruwa.
Mr Abang, a hukuncinsa, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda doka ba ta bashi damar zartar da hukuncin da ya so ba domin nuna munin laifin da satar man fetur ke kawo wa a Najeriya.
Ya ce sasancin da mai karar da wanda aka yi karar suka yi ya daure hannun kotu, domin a yanzu kawai N2000 za su biya su tafi.
Ya kuma koka kan yadda masu karar suka amince su saki jirgin ruwan bayan an biya Naira miliyan 5, inda ya ce abin da ya dace shine a mika wa gwamnatin tarayya ta yi gwanjonsa.
Umurni
Bisa tsarin sasancin da suka yi, wanda ya ce ba shi da ikon rashin amincewa da shi, Mr Abang ya umurci wadanda aka yi karar su 10 su biya tarar N20,000.
Ya kuma umurci jirgin ruwan ta biya Naira milyan 5 kamar yadda aka amince a sasancin.
Duk da hakan, alkalin ya bada umurnin a biya Naira miliyan 17 a matsayin riba da za a biya a asusun gwamnatin tarayya daga sayar da danyen man.
Ya ce kada a saki wadanda ake zargin har sai sun cika ka'idar da kotun ta saka.
Asali: Legit.ng