Da dumi-dumi: Tinubu ya dura Neja, ya shiga ganawa da IBB kan batun takara a 2023

Da dumi-dumi: Tinubu ya dura Neja, ya shiga ganawa da IBB kan batun takara a 2023

  • Bola Tinubu ya kai ziyara jihar Neja, inda ya gana da janar Ibrahim Badamasi Babangida a gidansa yau Alhamis
  • Rahotanni sun ce, da isowar Tinubu ya zarce gidan IBB, inda suka shiga tattaunawar sirri kan batun takarar Tinubu a 2023
  • A baya-bayan nan Bola Ahmad Tinubu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara, ya fara ziyartar jiga-jigan Najeriya

Minna, Neja - A yammacin ranar Alhamis ne tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kai ziyara Minna, babban birnin jihar Neja domin ganawa da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida (rtd).

Tinubu, shugaban jam’iyyar APC na kasa ya isa gidan Janar Babangida da misalin karfe 2:30 na rana, inda su biyun suka shiga wani taro kai tsaye bayan zuwansa.

Tibunu ya gana da IBB
Da dumi-dumi: Tinubu ya dura Neja, ya shiga ganawa da IBB kan batun takara a 2023 | Hoto: bbc.com
Asali: Depositphotos

Ziyarar da Tinubu ya kai wa Janar Babangida (rtd) wanda aka fi sani da IBB ya yi ta ne bayan ganawa da wasu jiga-jigan shugabanni a Najeriya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Najeriya ba ta buƙatar shugaban ƙasa na ƙabilanci, Hakeem Baba-Ahmed

Tinubu ya gana da wasu ‘Yan Arewa, ya fadi abinda ya ke jira ya ayyana takarar Shugaban kasa

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yace ba zai watsawa masu kiran ya yi takarar shugabacin Najeriya kasa a ido ba.

A ranar Talata, 14 ga watan Disamba, 2021, Daily Trust ta rahoto cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya gana da kungiyar Northern Alliance Committee.

An yi wannnan zama ne a birnin tarayya Abuja, inda aka cigaba da kira ga tsohon gwamnan na jihar Legas ya nemi kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Shi kuwa Bola Ahmed Tinubu ya nunawa magoya bayansa cewa zai iya amsa kiraye-kirayen na su.

A wani labarin, wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar a karkashin kungiyar Progressive Youth Movement (PYM), sun shigar da karar uwar jam’iyyar a gaban kotu.

Kara karanta wannan

'Dan marigayi Abacha na shirin shiga APC ne? Babban Sanatan APC ya magantu, ya wallafa hotunansu tare

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 13 ga watan Disamba, 2021, kungiyar Progressive Youth Movement na neman ta kawowa zaben APC cikas.

Matasan su na so kotu ta tsige kwamitin rikon kwarya da shirya zabe wanda Mai Mala Buni yake jagoranta. Sannan ta na so BOT ta kira zaben shugabanni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.