Luguden Wuta: Yan sanda sun yi magana kan wurin da Bello Turji ya koma bayan tserewa daga Zamfara

Luguden Wuta: Yan sanda sun yi magana kan wurin da Bello Turji ya koma bayan tserewa daga Zamfara

  • Rundunar yan sanda ta jihar Kwara ta musanta ikirarin ɗan majlisar wakilan tarayya game da gawurtaccen ɗan bindiga, Bello Turji
  • Ɗan majalisar ya bayyana cewa luguden wutan sojojin Najeriya ya sa Turji ya tsere daga Zamfara, ya kafa sansani a dajin Kwara
  • Kwamishinan yan sanda ya bada umarnin fara aikin sintiri na tsawon awanni 24 domin kare rayukan al'umma a jihar

Kwara - Hukumar yan sanda reshen jihar Kwara ta bayyana cewa ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji, da ya tsero daga jihar Zamfara bai shigo yankin dazukan Kwara ba.

Kakakin yan sanda na jihar, SP Ajayi Okasanmi, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, kamar yadda Jaridar Ripples ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Baicin kwarewar Buhari, da Najeriya ta ruguje kurmus

Yace ya zama wajibi hukumar yan sanda ta fito ta yi ƙarin haske kan maganar da mamban majalisar dokokin tarayya ya yi, wanda ya zargi cewa Turji, ya koma wani daji a cikin jihar Kwara.

Jihar Kwara
Luguden Wuta: Yan sanda sun yi magana kan wurin da Bello Turji ya koma bayan tserewa daga Zamfara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Okasanmi, ya nuna rashin jin daɗinsa kasancewar ɗan majalisar bai bayyana ainihin dajin ba bare ya tabbatar da abin da yake ikirari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

PM News ta rahoto Kakakin yan sandan na cewa:

"Baki ɗaya iyakokin dake jihar na cikin ƙasa da kuma na ƙasashen waje suna cikin tsaro a hannun yan sanda da kuma dakarun sojin Najeriya."
"Yan Bijilanti da Mafarauta suna aiki ba dare ba rana da haɗin guiwar hukumomin tsaro domin tabbatar da an sa ido kan me ke wakana a dazukan Kwara kuma a tsare su."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka domin kare shigowar ɗan bindigan?

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun bindige Basarake a jihar Arewa har lahira a cikin gidansa

Mista Okasanmi, ya ƙara da cewa a ranar Talata, kwamishinan yan sandan jihar Kwara, ya bada umarnin fara aikin sintiri na awanni 24 a dukkan iyakokin shige da ficen jihar.

Yace an ƙara wa jami'ai na musamman ƙarfi ta hanyar kara musu motocin sintiri da sauran kayan aikin da zasu taimaka musu a aikin su.

Ya kuma roki al'umma su cigaba da harkokin kasuwancin su na yau da kullum ba tare da wani ɗar-ɗar ba, inda ya tabbatar musu cewa Kwara na cikin tsaro.

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun kai mummunan hari hedkwatar APC, sun halaka jiga-jigan jam'iyya, sun sace mutum ɗaya

Yan ta'addan sun yi wa jiga-jigan jam'iyyar ɓarna, inda suka kashe mutum biyu, kuma suka jikkata wasu da dama, suka yi awon gaba da mutum ɗaya.

Wata majiya daga cikin mahalarta taron, ya bayyana cewa an kira taron ne domin sasanci tsakanin bangarorin jam'iyyar APC a kokarin da ake na haɗa kai baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Kebbi: Rayuka 15 ne suka salwanta a farmakin ƴan ta'adda, Jami'ai

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262