'Yan bindiga da ke gudun ceto rai su na kai farmaki yankunan Zamfara, Dan majalisa

'Yan bindiga da ke gudun ceto rai su na kai farmaki yankunan Zamfara, Dan majalisa

  • Dan majalisar tarayya mai wakiltar Gummi da Bukkuyum a jihar Zamfara, Sulaiman Abubakar Gumi, ya ce fatattakar ‘yan bindiga ne ya ke janyo hare-haren da suke kai wa
  • Ya ce misalin hakan shi ne hare-haren da suka kai garin Anka da Bukkuyum a makon farko na watan Janairu wanda suka halaka mutane da dama
  • Ya ce ragargazar da sojin sama suka yi wa dajikan da ke kewaye da jihar Zamfara ya sa ‘yan bindigan da ke zama cikin su suka tsero cikin gari don cutar da jama’a

Zamfara - Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum na jihar Zamfara, Sulaiman Abubakar Gumi ya ce korar ‘yan bindiga ne ke kawo hare-hare a garuruwa.

A cewar dan majalisar, harin da suka kai Anka da Bukkuyum a makon farko na watan Janairu ne misalin irin harin, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu yan bindiga maza suke kashewa a Zamfara, In ji Gumi

'Yan bindiga da ke gudun ceto rai su na kai farmaki yankunan Zamfara, Dan majalisa
'Yan bindiga da ke gudun ceto rai su na kai farmaki yankunan Zamfara, Dan majalisa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A cewarsa, aman wutar da sojin sama suka yi wa dajikan da ke makwabtaka da Zamfara ta janyo ‘yan bindigan suna tserewa don shiga garuruwa inda suke kai wa jama’a farmaki.

A baya Gumi ya taba gabatar da wani bayani a kan yadda ‘yan bindiga suka dinga kai hari da yawan su tsakanin 5 da 6 ga watan Janairun 2022, har suka halaka mutane 36 a Bukkuyum da kuma wasu 22 a karamar hukumar Anka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya ce sun banka wa kauyuku wuta da wasu garuruwa kamar Rafin Danya, Kurfa da Rafin Gero.

Dan majalisar ya kara da cewa, ‘yan bindiga sun yi barazanar kai farmaki garuruwa kamar Daki Takwas, Birnin Tudu, Leshi da Gambanda Magero matsawar ba su biya harajin da suka kallafa musu ba.

Ya yaba da aikin sojojin sama amma ya bukaci a kai jiragen yaki kamar Super Tucano zuwa Zamfara don yakar ‘yan ta’addan.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Buhari ya ba sojoji umurnin yin gaggarumin aiki a wata jihar Arewa

Zamfara APC: Rikici ya dauka sabon salo, ana amfani da 'yan daba wurin kai farmaki

A wani labari na daban, Rikicin cikin gida na cigaba da rincabewa a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta jihar Zamfara inda sabon salo ya kunno kai a cikin tsagi daban-daban na jam'iyyar ta yadda ake daukar nauyin kai farmaki da 'yan daba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, tsagin tsohon gwamna Abdulaziz Yari ya nuna firgici da tashin hankali a jihar inda suke zargin za a mayar da jam'iyyar filin daga inda 'yan daba ke baje-kolin su.

Shugaban tsagin, Lawal M. Liman, wanda ya yi wannan hasashen, ya bayyana cewa, farmakin kwanan nan da aka kai wa shugaban fannin yada labarai na kafafen sada zumuntan Sanata Kabiru Gwarba Marafa na jam'iyyar, Malam Shamsu Shehu datsakar rana ya zama abun tashin hankali ga duk mai san zaman lafiya da kiyaye doka a jihar.

Kara karanta wannan

Neja: Ƴan bindiga sun ɗaure ni, ina kallo suka kashe ƴaƴa na 6 ɗaya bayan ɗaya, Dattijo mai shekaru 75

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng