Dalibin sakandare ya gayyato mahaifiyarsa da ƴan daba sun lakaɗa wa malamansa duka don an umurci ya yi aski
- Dalibin makarantar sakandare da taimakon mahaifiyar sa da wasu ‘yan daba sun lakada wa malaman sa dukan tsiya saboda sun umarce sa da ya yi aski
- An samu bayanai akan yadda ‘yan daban suka afka makarantar Toyin da ke Ere a Ado-Odo cikin jihar Ogun inda suka dinga dukan malaman kamar Allah ya aiko su
- Dalibai suna ci gaba da cutar da malamansu duk da kafin makaranta ta ba dalibai gurbin karatu sai iyayensu sun sanya hannu a takarda saboda gudun irin hakan
Jihar Ogun - Wani dalibi a wata makarantar sakandare da taimakon iyayensa da wasu ‘yan daba sun lakada wa malaman sa dukan tsiya saboda umartar shi da yin aski, Daily Trust ta ruwaito.
An samu bayanai akan yadda ‘yan daban suka afka makarantar sakandaren Toyin da ke Ere, Ado-Odo, cikin Jihar Ogun don cutar da malaman.
Dalibai suna ci gaba da cutar da malamansu a jihar Ogun duk da yadda makarantu suke bukatar iyaye su sanya hannu a fom kafin su ba dalibai gurbin karatu.
Daily Trust ta ruwaito yadda a karshen shekarar 2021 dalibai suka gayyaci wasu batagari har makarantar su don lakada wa malamansu duka.
Malaman sun kori dalibin ne bayan sun ga askin da ya yi ba yi da kyau
Sai kuma ranar Talata, saboda malaman sun umarci dalibin ya aske wani mummunan aski da ya yi, shi da mahaifiyarsa suka yi hayar ‘yan daba inda suka afka har makarantar da ke Ado-Oda a karamar hukumar Ota cikin jihar inda suka ji wa malamai uku raunuka.
Wakilin Daily Trust ya tattaro bayanai akan yadda makarantar ta dakatar da Joshua Joseph daga shiga makarantar saboda askin sa.
Wani malami Mr Kabir Azeez ya bukaci dalibin ya je ya aske gashin shi kafin ya ba shi damar shiga aji.
Amma Joshua ya koma makarantar daga bisani ya koma makarantar da mahaifiyar sa da wasu ‘yan daba don su zane malamai.
Wata majiya ta ce:
“Malaman da aka zane sun hada da Messrs Abel Thomas, Kabir Azeez da Adegun Adekunle. Daya daga cikin ‘yan daban, Posu Baale ya fasa gilashin motar Mr Jolayemi Jeromu.”
Mataimakiyar shugaban makarantar, Mrs Mariam ta tabbatar da aukuwar lamarin.
Tare da mahaifiyar suka zane malaman
Inda ta ce:
“A ranar Litinin muka umarci dalibinmu da ya je ya aske gashin sa don askin nasa ba na mutunci bane. A jiya (Talata) na amshi jakar sa sannan muka ce ya dawo idan ya aske kan.
“Dawowar da zai yi sai ga shi da wasu maza biyu da mata biyu suna tambayar mu abinda yasa muka ce ya aske kan. Daga nan na ce su fita daga ofishi na idan har bai yi aski ba. Na ba su jakar shi nace su je gida su koyar da shi a gida.
“Bayan wucewar su ne naji hayaniya a tsakar makaranta suna dukan malamai har da fasa gilashin wata mota da ke tsakar makarantar.”
‘Yan sanda sun kama ‘yan daban
Ta kara da bayyana yadda suka dawo suna zargin malaman makarantar da sace musu waya daga nan hukumar makarantar ta kira ‘yan sanda wadanda suka kama ‘yan daban suka rufe su.
Daily Trust ta nemi zantawa da Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi inda ya ce bai san komai ba dangane da lamarin.
Sai dai ya yi alkawarin tuntubar wakilin Daily Trust idan ya samu bayanai.
Iyaye suna sa hannu a wata takarda wacce za su amince da dokokin makaranta sannan su tabbatar yaransu ba su gwada wata dabi’ar assha ba a makaranta.
Wakilin Daily Trust ya samu takardar da mahaifin yaron da ya yi aika-aikar, Joshua Sunday ya sa hannu da alkawarin yaron sa zai kasance mai ladabi da biyayya ga hukumar makarantar.
Asali: Legit.ng